Ahmad Adamu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ahmad Adamu
Rayuwa
Haihuwa Katsina, 3 ga Maris, 1985 (39 shekaru)
ƙasa Najeriya
Mazauni Katsina
Karatu
Makaranta Newcastle University (en) Fassara
Sana'a

Ahmed Adamu masanin tattalin arzikin man fetur kuma malamin Jami'a ne a Najeriya. An zabe shi a ranar 12 ga watan Nuwamba, 2013 a matsayin shugaba na farko a duniya na Majalisar Matasa ta Commonwealth (CYC). Adamu ya kasance shugaban CYC har zuwa watan Maris 2016.

Adamu ya wakilci kasarsa a shirye-shiryen matasa na kasa da kasa da na Commonwealth, kuma yana cikin manyan jigon majalisar matasan Najeriya. Adamu masanin tattalin arzikin man fetur ne, malamin jami'a, marubuci, kuma mai magana mai karfafa gwiwa. Shi kwararre ne kan jagoranci da ci gaban mutum, kuma ya horar da kwararru da matasa kan jagoranci da ci gaban mutum, shi ma kwararren kocin kwakwalwa ne. Dokta Ahmed Adamu ya rubuta kuma ya buga jerin littattafai goma kan jagoranci da ci gaban mutum. A karshen shekarar 2018, an nada shi a matsayin mataimaki na musamman kan harkokin matasa da dabaru ga tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar. Ya tsaya takarar dan majalisar wakilai ta tarayya, mai wakiltar mazabar Katsina ta tsakiya a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP na 2018, amma ya sha kaye a zaben fidda gwani.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]