Ajwad bin Zamil

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ajwad bin Zamil
Rayuwa
Haihuwa 1418
ƙasa Jabrids (en) Fassara
Mutuwa 1496 (Gregorian)
Ƴan uwa
Yara
Sana'a
Yankin Tsbirin Larabawa


Ajwad bin Zamil bin Saif Al-Uqaili (1418 - 1496 Miladiyya) sarki ne wanda ya mulki kasashen gabashin tsbirin larabawa da ya hada da Ahsa' da Bahren. Yayi mulki ne karkashin daular da aka fi sani da "Al-imarah Al-Jabriyya".[1]

Nasabarshi[gyara sashe | gyara masomin]

Sunanshi Ajwad bin Zamil bin Saif Al-Uqaili Al-jabri. Ya shahara ne da sunan Ibn Jabr (Dan Jabr) saboda sunan kakanshi. Kuma dan asalin yankin Najd ne tare da kuma kasancewa akan mazjabar malikiyya.

An haife shi a garin Alhasa a watan Ramadan shekara ta 1418 Miladiyya.[2]

Rayuwarshi[gyara sashe | gyara masomin]

Sultan Ajwad bin Zamil al-Jabri ya kasance mai addini, kuma yana da dabi'ar karantar fikihu. Hakan yasa ya jajirce wajen gudanar da ayyukan addinin Musulunci, kamar sallar Juma'a da halartar jam'i, kuma ya yi aikin Hajji fiye da sau daya.

Siffofinsa[gyara sashe | gyara masomin]

Yawancin littafan da suka yi bayani akan rayuwar Sarki Ajwad suna nune cewa ya kasance mutum ne mai kyawawan dabi'u. Sannan ya shahara a fagen hawan doki da yawan kyauta.

Wasu manazarta sun bayyana shi a matsayin daya daga cikin shahararrun sarakunan da suka yi suna, wadanda suka bambanta da karamci, da kyawawan halaye, irin na Larabawa wanda ke iya ba da abin da suke da shi da abin da suka mallaka don girmama bako, da ba shi hakkinsa, wanda hakan nema yasa suka zama abin koyi a wajen karamci. Haka nan Sarki Ajwad ya yi fice wajen hakuri, da juriya akan abinda ya shafi mazhaba a addini, watakila abin da ke tabbatar da haka shi ne, ya yi kuma amfani da wasu malaman fikihu Ahlus-Sunnah bayan sun kasance ya Shi’a. Da yake Sarkin Ajwad ya kasance mafificin masu iya hawan dawaki, ya jajirce wajen yaki. Marubutan tarihi sun shaida cewa wannan sarkin yana da halaye masu kyawun gaske.

Hawansa Mulki[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta sun yi ssabani akan sherar da sarki Ajwad ya hau karagar mulki. Hakan yasa wasu daga cikin su suka fi karkata kan cewa ya hau mulki ne a shekara ta 875 (Hijriyya) wanda yayi daidai da shekarar 1470 miladiyya.

Masarautarsa ​​ta kasance a farkon karni na goma, kamar yadda ta kasance a ƙauyen Al-Manizla, a cikin Al-Ahsa a yau, kuma fadarsa tana yamma da ƙauyen da ake da su har zuwa yanzu.

A shekara ta 912 bayan hijira Ibn Zamil ya yi hajjin taron fiye da dubu talatin.

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Sarki Ajwad bin Zamil ya rasu a shekara ta 1496 M, sannan dan cikinsa Muhammad shi ya gaje shi.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. السخاوي، شمس الدين (1992)، الضوء اللامع لأهل القرن التاسع ط1 بيورت لبنان
  2. علي بن غانم الهاجري (2018) السلطنة الجبرية في عهد السلطان أجود بن زامل، دار جامعة حمد بن خليفة للنشر، ص33