Jump to content

Alƙali Abubakar Salihu Zaria

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Abubakar Salihu Zariya wanda aka fi sani da Alƙali Zariya babban Malamin Addinin Musulunci ne, (An haife shi ranar 1 ga watan Janairu shekara ta 1980) a unguwar Tudun Wada cikin birnin Zariya a Jihar Kaduna.[1]

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Alƙali Abubakar Salihu Zariya a unguwar Tudun Wada cikin birnin Zariya a Jihar Kaduna.

Ya fara karatu a makarantar Isah Abdulkarim Nursery and Primary School, kafin ya samu shaidar digirin sa ta farko a Jami'ar Ahmadu Bello inda ya karanta fannin Addinin Musulunci (Islamic Studies).

Cikin Malaman da ya yi karatu a hannusu, akwai mahaifinsa da Mallam Umar a Tudun Wadan Zariya da Mallam Aminu Adam Nepu, masanin Fikihu da Nahawu, akwai Mallam Mai Bala'i Gyallesu da Mallam Shu'aibu Salihu Zariya.

  1. https://www.bbc.com/hausa/articles/c1d73xp3380o.amp