Alabi Hassan Olajoku

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Alabi Hassan Olajoku
Rayuwa
Haihuwa 1947
Mutuwa 15 Mayu 2005
Karatu
Makaranta George Washington University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da ɗan kasuwa

Alhaji Alabi Hassan Olajoku (1947–2005) ɗan kasuwa ne a Najeriya, kuma ɗan siyasa, wanda wasu da ba a san ko su wanene ba suka kashe shi, a ranar 15 ga watan Mayun shekara ta 2005.[1]

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Alabi Hassan Olajoku a ranar 9 ga watan Fabrairu, 1947, a Mushin, Jihar Legas, ga dangin Aristocratic na Alhaji Kehinde Asani Olajoku (Ile Oloosa Oko), na Isale Imole, llobu, Jihar Osun. Mahaifinsa ya zauna a Waigbo, wani yanki mai ban sha'awa na Mushin.

Asani Olajoku ya kasance wani babban jigo a harkar sufuri da aka tsara a birnin Legas, kuma yana ɗaya daga cikin manyan masu safara tsakanin farkon shekarun 1950 zuwa 1970, ya mallaki daya daga cikin manya-manyan motoci ƙirar (BOLEKAJA). Shi ne Ekerin na Waigbo, Mushin, Lagos, Nigeria. Alabi Hassan Olajoku shi ne ɗa na farko.

A 1959 Alhaji Hassan Olajoku ya shiga makarantar firamare a makarantar Mrs. F. Kuti's Class, Mallakar ƙwararriyar masaniyar ilimi, Mrs. Olufunmilayo Ransome Kuti.[2]

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Alhaji Alabi Hassan Olajoku ya halarci makarantar Ansaru-deen Grammar School da ke lamba 63 Randle Avenue, Surulere, Legas, inda ya fara karatunsa na sakandire daga 1964 zuwa 1968. A shekarar 1972, Alhaji ya tafi ƙasar Amurka, sannan ya halarci Kwalejin Al'umma ta North Virginia dake Alexandria, Virginia, inda ya samu digiri a fannin kasuwanci, daga nan kuma ya samu digiri na biyu a fannin kasuwanci, Har-wayau ya kuma samu gurbin karatu a Jami'ar George Washington, Washington DC (Karkashin tallafin Gwamnatin Jihar Legas), sannan ya samu. BBA ( Bachelor of Business Administration ) a fannin kuɗi a shekarar 1976. Ya kammala karatunsa na digiri na biyu a fannin kasuwanci a jami’a, inda ya karanta MBA (Finance and Investment) a shekarar 1978, kafin ya dawo Najeriya a shekarar 1979 domin yin hidimar matasa na ƙasa a ƙasar da basu wuce shekara 30 da haihuwa ba. Hassan ya ci gaba da kasancewa a cikin jerin shugaban a duk zaman da ya yi a Jami'ar George Washington.

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 1970 Alhaji Hassan ya samu aiki a sashen ketare na National Bank of Nigeria Limited akan Broad street (Banuso House), Lagos, Nigeria. 

A shekarar 1983, Alhaji Hassan ya sha ruwa a kamfanin sa na Gudanar da Shawarwari. Ɗaya daga cikin kamfanoninsa, Constructive Alternative Limited, ya kasance sanannen mashawarcin masu ba da shawara kan haraji zuwa Legas, Ribas da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Alhaji Alabi Hassan Olajoku shi ne shugaba kuma wanda ya kafa rusasshen bankin Mushin Central Community.

Kamfanonin nasa sun hada da Lone Star Consulting Limited, Hassan-Olajoku Construction Limited, Hassan-Ola Consultancy da Paramo Development Ventures.[3]

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Alhaji Alabi Hassan Olajoku ya shiga harkokin siyasa a shekarar 1987 ƙarƙashin rusasshiyar jam’iyyar sifiri ta gwamnatin mulkin soja ta Janar lbrahim Babangida.

Ya kasance sakataren rusasshiyar jam'iyar NRC ta jihar Legas, Najeriya da ya taimaka wajen kafa jam'iyyar Alliance for Democracy (AD).[4]  Wani abin burgewa ne ganin yadda irin siyasar da suka shuka tun daga lokacin ta yi tsiro zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a yanzu jam’iyya ce mai karfi wacce ta sauya fasalin siyasa da tattalin arziki a Najeriya.

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Alhaji Hassan Olajoku Musulmi ne mai tsoron Allah kuma ya riƙe mukaman addinin Musulunci kamar su Baba Adeeni na Ilobu[5] Jihar Osun da kuma Oganla Adeeni na Alakuko, Jihar Legas

Alhaji Alabi Hassan Olajoku mutumin iyali ne. Yayi aure da Hon. Fausat Hassan Olajoku.[6]  

Ya haifi ƴaƴa shida ƴaƴan da su ka haɗa da; Ajibade Olajoku, Babatunde Hassan Olajoku, Dr. Folawiyo Kareem Olajoku,[7] Abisoye Mojeed Olajoku, Toyosi Olajoku da Omoboroji Fasilat Olajoku. 

Bayan nan, Kafin a kashe shi[gyara sashe | gyara masomin]

Fitaccen dan Iobu Land ne kuma mai alfahari, ya kasance a sahun gaba wajen bunƙasa jihar Osun ta kowane fanni da suka haɗa da samar da ababen more rayuwa, noma, ilimi, masana'antu da siyasa. A ci gaba da gudanar da wannan mugunyar hangen nesa da kuma fafutukar neman kuɗi da dabarun zaben Rauf Aregbesola a matsayin gwamnan jihar Osun, wasu ƴan bindigar da ba a san ko su wanene ba, suka kashe shi a ranar 15 ga watan Mayu, 2005, a mahadar Gbongan, jihar Osun, yana da shekaru 58 a duniya.[8]

Don tunawa da shi[gyara sashe | gyara masomin]

Rauf Aregbesola ya zama gwamnan Osun a ranar 26 ga Nuwamba, 2010. wanda aka ce ya yi wa Alabi Hassan Olajoku rai, cewa bai mutu a banza ba. Rauf Aregbesola ya gina wurin shakatawa na duniya a daidai wurin da aka kashe shi don tunawa da shi, wurin an saka masa sunan: Hassan Olajoku Park Gbongan.[9]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Aregbesola Unveils Park In Honour Of Late Hassan Olajoku • Channels Television". Channels Television. 2013-05-17. Retrieved 2017-05-25.
  2. "Funmilayo Ransome-Kuti biography | Women". en.unesco.org (in Turanci). Retrieved 2017-05-25.
  3. "Ladipo Market Crises Deepen". PM NEWS Nigeria. 2011-01-04. Retrieved 2017-05-25.
  4. Ugah, Hammed Shittu And Ndubuisi (2005-05-17). "Nigeria: 'How AD Financier Was Killed'". This Day (Lagos). Retrieved 2017-05-25.
  5. "The Nation September 13, 2011". issuu (in Turanci). Retrieved 2017-05-25.
  6. Voice, City. "'We are working to bring development to Ojokoro' – Fausat Olajoku | City Voice Newspaper". cityvoiceng.com (in Turanci). Archived from the original on 2019-10-21. Retrieved 2017-05-25.
  7. "Osun: Time To Decide". The Official Website Of The State Of Osun. 2014-07-31. Archived from the original on 2017-07-06. Retrieved 2017-05-25.
  8. Ugah, Hammed Shittu And Ndubuisi (2005-05-17). "Nigeria: 'How AD Financier Was Killed'". This Day (Lagos). Retrieved 2017-05-25.
  9. "Aregbesola Celebrates Slain Political Associate With Ultra Modern Rest Station". PM NEWS Nigeria. 2013-05-16. Retrieved 2017-05-25.