Ali Gazi
Ali Gazi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 15 century |
Mutuwa | 1487 |
Sana'a | |
Sana'a | ruler (en) |
Wurin aiki | Afirka ta Yamma |
Ali Gazi, Ali Gaji Dunamami ibn Zeinab, ko Ali ibn Dunama, yakasance Sarkin Daular Bornu daga shekarar alif dubu daya da dari hudu da saba'in da shida 1476 har zuwa shekarar alif dubu daya da dari biyar da ukku 1503 ko shekarar alif dubu daya da dari biyar da bakwai 1507. [1][2][3]
Gabda fara mulkinsa, sai gidan sarautar Sefuwa ta rabu gida biyu na masu mulki. Sakamakon makullata dake masarautar da fadan cikin gida. Ya hada kan masarautar sa ta hanyar kashe sarkin dake ikirarin sarauta na dayan bangaren sannan ya hana wani yasake neman sarautar.
Ali Gazi ya kuma dauki makiwatan Bulala wadanda suka korar masa mutane daga Kanem lokacin da Daular Kanem tayi taushi. Ya samu galaba akansu kuma ya kwato tsohon birnin daular Kanem, Njimi. Ya kuma sake kafa sabuwar birni a Birnin Gazargamu.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Urvoy, Y. (1949). Historie De L'Empire Du Bronu (Memoires De L'Institut Francais D'Afrique Noire, No. 7 ed.). Paris: Librairie Larose. p. 56.
- ↑ Palmer, Richmond (1936). The Bornu Sahara and Sudan. London: John Murray. pp. 94, 222–225.
- ↑ Barth, Henry (1890). Travels and Discoveries in North and Central Africa. London: Ward, Lock, and Co. p. 361. Retrieved 10 March 2019.