Ali Muhammad Khan
|
| |||||||
1 ga Yuni, 2013 - District: NA-10 (Mardan-II) (en)
29 ga Yuli, 2022 District: NA-22 Mardan-III (en) | |||||||
| Rayuwa | |||||||
| Haihuwa |
Mardan District (en) | ||||||
| ƙasa | Pakistan | ||||||
| Harshen uwa | Urdu | ||||||
| Karatu | |||||||
| Harsuna | Urdu | ||||||
| Sana'a | |||||||
| Sana'a | ɗan siyasa da lauya | ||||||
| Imani | |||||||
| Jam'iyar siyasa |
Pakistan Tehreek-e-Insaf (en) | ||||||
Ali Muhammad Khan
| |
|---|---|
| علی محمد خان | |
Khan a 2024
| |
Ali Muhammad Khan (an haife shi 30 Nuwamban shekarar 1979) ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya yi ministan harkokin majalisa daga 17 Satumba 2018 zuwa 10 Afrilun shekarar 2022. A halin yanzu mamba ne a Majalisar Dokokin Pakistan tun Fabrairu 2024. Ya taɓa zama memba daga Agustan shekarar 2018 har zuwa Yuli 2022.
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Khan a ranar 30 ga Nuwamban shekarar 1979 a cikin dangin Pashtun a Mardan, Khyber Pakhtunkhwa . [1]
Kakansa Khan Pir Muhammad Khan ɗan gwagwarmayar Pakistan ne kusa da Muhammad Ali Jinnah, kuma a cikin shekara ta 1940 ya jagoranci ayarin Mardan don halartar ƙudurin Lahore . Ya kuma taɓa zama ministan tarayya har sau biyu, to amma bayan shi dangi ko kaɗan sun daina shiga harkokin siyasar ƙasa. [2]
Khan ya sami digirin sa na LLB daga Kwalejin Universal Islamabad (UCI), inda ya shiga can bayan Barista Masroor Shah, babban lauya na Kotun Koli ya ba shi shawara. [3]
Shi ma injiniyan farar hula ne ta fannin sana'a. [4]
Sana'ar siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]An zaɓe shi a Majalisar Dokokin Pakistan a matsayin dan takarar PTI daga mazabar NA-10 (Mardan-II) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2013. Ya samu ƙuri'u 46,531 sannan ya doke ɗan takarar JUI-F . [5]
An sake zaɓe shi a Majalisar Dokoki ta ƙasa a matsayin ɗan takarar PTI daga mazaɓar NA-22 (Mardan-III) a babban zaben Pakistan na shekarar 2018. ya samu ƙuri'u 58,577 sannan ya doke Moulana Mohammad Qasim . [6]
A ranar 17 ga Satumban shekarar 2018, an shigar da shi cikin majalisar ministocin tarayya na Firayim Minista Imran Khan a matsayin karamin ministan harkokin majalisa . [7] Yayin da yake rike da mukamin minista, ya gabatar da wani kuduri ga Majalisar Dokokin Pakistan da ke neman a rataye jama'a na masu fyade da masu cin zarafi, duk da cewa wannan ƙudurin ya janyo suka a matsayin take haƙƙin ɗan Adam ga masu laifi daga ƴan majalisar adawa da Amnesty International . An zartar da kudurin ne duk da cewa wasu 'yan siyasar gwamnati da suka haɗa da Shireen Mazari da Fawad Chaudhry sun nuna adawa da shi. [8] [9]
A ranar 11 ga Mayun shekarar 2023, hukumomin Pakistan sun kama shi a ƙarƙashin Dokar Kula da Jama'a (MPO) saboda zargin hannu da tunzura shi a zanga-zangar Pakistan na 2023 . Bayan samun beli tare da sake kama shi sau takwas daban-daban, kuma ya shafe kwanaki 78 a gidan yari, a ranar 27 ga watan Yuli, an sake shi bayan da babbar kotun Peshawar (PHC) ta shiga tsakani don bayar da belinsa. [10] [11]
An zaɓe shi a matsayin memba na Majalisar Dokokin Pakistan a karo na uku a babban zaɓen Pakistan na 2024 daga NA-23 Mardan-III a matsayin dan takara mai zaman kansa mai goyon bayan PTI . Ya lashe zaben kuma ya samu ƙuri'u 102,188 yayin da Ahmad Khan na jam'iyyar ANP ya zo na biyu ya samu kuri'u 32,655. [12] A matsayinsa na dan majalisar wakilai ta kasa (MNA) ya soki gwamnatin Shehbaz Sharif da hukumomi kan sace manyan mambobin PTI. [13]
Rigingimu
[gyara sashe | gyara masomin]Cin zarafi da 'yan sanda
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 2014, an yi wa Khan rajistar karar ƴan sanda bayan da ya kai hari ofishin 'yan sanda wanda ya yi sanadin jikkata 'yan sanda uku. ciki
Barazana ga masu kishin addini
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin shekarar 2017, Khan ya tabbatar da cewa wadanda ke son mayar da Pakistan saniyar ware su "gyara hanyoyinsu ko kuma su bar ƙasar", saboda shi Pakistan ana nufin ko da yaushe ta zama ƙasar Musulunci.[14]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Detail Information". www.pildat.org. PILDAT. Archived from the original on 25 April 2017. Retrieved 24 April 2017.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
- ↑ "Meri Kahani [My Life-Story]". PakVoter:Civic Information Portal. Archived from the original on 28 June 2023.
- ↑ "UCI's alumni profile". Universal College Islamabad. 7 September 2021. Archived from the original on 28 June 2023.
- ↑ "Two Historical and Monumental Resolutions Presented by Engineer Ali Muhammad Khan, Minister of State for Parliamentary Affairs & InCharge Prime Minister's Public Affairs & Grievances wing". Pakistan Meteorological Department. Archived from the original on 26 August 2023.
- ↑ "2013 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 1 February 2018. Retrieved 1 April 2018.
- ↑ "NA-22 Result - Election Results 2018 - Mardan 3 - NA-22 Candidates - NA-22 Constituency Details - thenews.com.pk". www.thenews.com.pk (in Turanci). Retrieved 1 August 2018.
- ↑ "Six federal ministers inducted into cabinet". 12 September 2018.
- ↑ "Pakistan Parliament passes resolution demanding public hanging of child sexual abusers". The Indian Express (in Turanci). 2020-02-07. Retrieved 2024-10-19.
- ↑ "Pakistan: Public hangings are acts of unconscionable cruelty". Amnesty International (in Turanci). 2020-02-07. Retrieved 2024-10-19.
- ↑ "PTI's Ali Muhammad Khan, Ejaz Chaudhry arrested as crackdown intensifies". Geo.tv (in Turanci). 2023-05-11. Retrieved 2023-07-27.
- ↑ "PTI leader Ali Muhammad Khan released from jail". Samaa (in Turanci). 2023-07-27. Retrieved 2023-07-27.
- ↑ "NA-23 Election Result 2024 Mardan 3, Candidates List". www.geo.tv (in Turanci). Retrieved 2024-10-19.
- ↑ "'May 9 for democracy': In fiery NA speech, PTI's Ali Muhammad Khan blasts govt for arresting party leaders". DAWN.COM (in Turanci). 2024-09-10. Retrieved 2024-10-19.
- ↑ Raja, Raza Habib (29 March 2017). "It is pretty clear that neither Ali Muhammad Khan nor PTI know why Pakistan was created". The Express Tribune. Retrieved 28 June 2023.