Jump to content

Ali Nikzad

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ali Nikzad
Member of the Islamic Consultative Assembly (en) Fassara


District: Ardabil, Nir, Namin and Sareyn (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Ardabil (en) Fassara, 22 Satumba 1954 (70 shekaru)
ƙasa Iran
Karatu
Makaranta Iran University of Science and Technology (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Shi'a
Ali Nikzad

Ali Nikzad Persian : (an haife shine a ranar 22 ga watan satumba shekara ta 1954 )ya kasance ɗan siyasan Iran,ne kuma ɗan siyasa mai ra'ayin mazan jiya kuma tsohon minista ne a majalisar ministoci ta Kasar Iran.

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]
Ali Nikzad

An haifi Nikzad a shekara ta 1961. Yana da digiri na farko a ci gaban birane daga Jami'ar Elm-va-san'at (Kimiyya da Masana'antu). Sannan ya sami digiri na biyu a fannin kula da jama'a daga Jami'ar Gudanar da Masana'antu. Akbar Nikzad ɗan'uwansa ɗan siyasan Iran ne kuma tsohon Gwamnan Lardin Ardabil.

An nada Nikzad gwamnan lardin Ardabil a shekara ta 2005. Sannan ya kasance darektan kungiyar kananan hukumomi a ma'aikatar cikin gida har zuwa shekara ta 2009. Ya yi aiki a matsayin Ministan Sufuri da Gidaje daga watan Agusta a shekarar 2009 zuwa Yunin shekarata 2011. Ya kuma kasance mukaddashin ministan hanyoyi da sufuri daga watan Fabrairu zuwa Yunin shekara ta 2011. A matsayinsa na ministan gidaje, ya maye gurbin Mohammad Saeedikia bayan sake zaben Shugaba Mahmud Ahmadinejad.

A ranar 7 ga watan Fabrairun shekara ta 2011, Ahmadinejad ya nada Nikzad a matsayin mukaddashin ministan hanyoyi da sufuri don ya gaji tsohon korarren Minista Hamid Behbahani. An nada Nikzad a matsayin ministan kula da kayayyakin more rayuwa a watan Mayu na shekara ta 2011 lokacin da aka kirkiro ma'aikatar, inda ya hada ma'aikatun gida biyu da na birane da tituna da sufuri. A karshen shekara ta 2012, an kuma nada shi mukaddashin ministan sadarwa da fasahar kere-kere. Shugaba Ahmedinejad ya ba shi shawarar zama ministan mukamin a watan Janairun shekara ta 2013. Sai dai kuma Majalisa ba ta amince da shi ba.

Ali Nikzad
Ali Nikzad

Ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2013. Sai dai kuma daga baya ya ki amincewa da takararsa. A watan Yunin shekarar 2013, an zabi Nikzad a matsayin dan takarar magajin garin na Tehran. Kungiyar "Viva bazara" wacce ta kunshi kawayen Ahmedinejad ba ta iya cin zaben kananan hukumomi ba wanda kuma aka gudanar a ranar 14 ga Yunin shekara ta 2013 a matsayin zaben shugaban kasa. Saboda haka, zaɓen Nikzad a matsayin magajin garin Tehran ya zama da wuya. A zaben shekara ta 2017, an nada shi a matsayin shugaban yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa Ebrahim Raisi.[1] However, he later declined his candidacy.[2][3][4][4][5][6]

  1. "Iran Election Watch 2013: Twenty four presidential candidates emerge". The International. 21 March 2013. Archived from the original on 6 June 2014. Retrieved 27 July 2013.
  2. "چه کسی کاندیدای نهایی دولت خواهد بود؟". IUS News. Retrieved 27 July 2013.
  3. "Censoring an Iranian Campaign Story". EA WorldView. 4 June 2013. Retrieved 27 July 2013.
  4. 4.0 4.1 "End of Ahmadinejad's "Viva Spring"". Anadolu Agency. Tehran. 17 June 2013. Retrieved 27 July 2013.
  5. "Ex-minister made Raisi campaign chief". 23 April 2017.
  6. "Is conservative Iranian candidate reviving Ahmadinejad's Cabinet?". 23 April 2017.