Mahmoud Ahmadinejad

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Mahmoud Ahmadinejad
Mahmoud Ahmadinejad 2009.jpg
Rayuwa
Haihuwa Aradan (en) Fassara, Oktoba 28, 1956 (63 shekaru)
ƙasa Iran
Mazaunin Narmak (en) Fassara
Yan'uwa
Karatu
Matakin karatu Master of Science in Engineering (en) Fassara
Sana'a
Sana'a university teacher (en) Fassara, ɗan siyasa da injiniya
Mamba Alliance of Builders of Islamic Iran (en) Fassara
Imani
Addini Shi'a
Jam'iyar siyasa Alliance of Builders of Islamic Iran (en) Fassara
Society of Devotees of the Islamic Revolution (en) Fassara
IMDb nm2258253
ahmadinejad.ir/
Mahmoud Ahmadinejad signature.svg

Tarihin Rayuwar Sabon Shugaban Kasar Iran Mahmud Ahmadi Nejad: An haifi Mahmud Ahmadi Nejad a kauyen Garamsar na jihar Samnan a shekarar 1956, mahaifinsa dai wani makeri da ke 'ya'ya bakwai, Ahmadi Nejad shi ne na hudu cikin yaran. Ahmade Nejad dai tun yana dan shekara guda a duniya iyayen nasa suka dawo birnin Tehran da zama. Ahmadi Nejad ya fara karatun firamare da sakandarensa ne a birnin Tehran din inda bayan nasarar da ya samu a jarabawar karshe ta sakandare ya wuce zuwa jami'ar birnin inda ya karanci ilmin harkar gine-gine har ya samu digiri na biyu a wannan fanni a shekarar 1966. Daga nan ya ci gaba da karantarwa a jami'ar da kuma ci gaba da karatunsa inda ya sami digirin-digirgir a 1977.

Ahmadi Nejad ya fara harkokin siyasa ne tun a jami;ar, wato tun kafin nasarar juyin juya halin Musulunci inda ya kasance daga cikin masu goyon bayan kiran da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya ke yi ta hanyar shirya tarurrukan addini da lakcoci kan mahangar Imam da kuma tafarkinsa, baya ga haka kuma ya kasance daga cikin masu yada takardu da lakcocin marigayi Imam din da ke kiran al'umma da suka tashi don kawar da gwamnatin kama-karya ta Shah, haka dai ya ci gaba da wannan aiki har bayan nasarar juyin juya halin.

Bayan nasarar juyin, an kafa wani kwamiti na 'yan jami'a da ke ganawa da marigayi Imam da tattaunawa kan mas'aloli daban-daban na siyasa da kuma abubuwan da suka shafi jami'a, an zabi Dr. Ahmadi Nejad a matsayin wakilin 'yan jami'an a wannan kwamiti kuma haka lamarin ya ci gaba har zuwa wannan lokaci.

Bayan kaddamar da hare-haren wuce-gona da iri da Saddam ya kaddamar kan Iran, wato kallafaffen yaki na shekaru 8, Ahmad Nejad ya kasance a sahun gaba-gaba a yayin wannan yaki, inda daga baya ma aka zabe shi daga cikin sojoji na musamman na dakarun kare juyin juya halin Musulunci da aka kafa da nufin kare juyin da kuma kasar Iran din gaba daya. Saboda irin kwarewar da yake da shi, an zabe babban jami'in tsare-tsare a bataliya ta 6 ta dakarun da ke alhakin kare yammacin kasar.

A bangare mukamai na siyasa da gwamnati kuwa, Ahmadi Nejad ya rike matsayin mataikamakin magajin garin Kurdistan, kana daga baya kuma aka nada shi a matsayin mai ba wa ministan al'adu da ilmi mai zurfi kan harkokin da suka shafi al'adu. Daga baya kuma an zabe shi a matsayin magajin garin Ardabil, sakamakon irin ayyukan ci gaban da ya gudanar an zabe shi a matsayin magajin garin da ya fi sauran takarorinsa gudanar da ayyukan ci gaba. Irin wannan kwarewa tasa tasa aka zabe shi a matsayin magajin garin birnin Tehran inda a nan ma ya gudanar da ayyukan gaske na ci gaban birnin da ake ganin na daga cikin dalilan da yasa al'ummar birnin suka zabe shi a wannan zabe na shugaban kasa da aka gudanar.

An shaidi Ahmadi Nejad da cewa mutum ne mai rayuwa cikin sauki da ya damu da halin da talakawa suke ciki, hakan ne ma ya sa wasu suke kwatanta shi da tsohon shugaban kasar Ali Raja'i da munafukai suka kashe. A bangaren harkokin addini kuwa, Ahmadi Nejad ya yi fuce wajen kula da koyarwa ta addini da kuma shiryar da na kasa da shi zuwa ga hakan. Dukkan wadannan ababe biyu su ma sun taimaka masa nesa ba kusa wajen janyo hankula al'ummar Iran zuwa gare shi.