Alinah Kelo Segobye

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Alinah Kelo Segobye
Rayuwa
ƙasa Botswana
Karatu
Makaranta University of Botswana (en) Fassara master's degree (en) Fassara
University of Cambridge (en) Fassara 1994) Doctor of Philosophy (en) Fassara
Matakin karatu Doctor of Philosophy (en) Fassara
Sana'a
Sana'a archaeologist (en) Fassara, gwagwarmaya da Farfesa
Employers University of Botswana (en) Fassara
Namibia University of Science and Technology (en) Fassara
Kyaututtuka

Alinah Kelo Segobye 'yar gwagwarmayar ci gaban zamantakewar al'umma ne kuma masaniya a ilimin kimiya na kayan tarihi, tare da ƙwarewa a fannin ci gaban zamantakewa da cutar kanjamau da kuma makomar nazarin abubuwan da suka gabata a Afirka da ilimin kimiya na Afirka.[1] Ita ce Shugabar sashen Kimiyyar Ɗan Adam a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Namibia kuma zaɓaɓɓiyar fellow na Kwalejin Kimiyya na Afirka.

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Segobye ta kammala karatun digirinta na farko da digiri na biyu a Jami'ar Botswana, kuma ta kammala karatun digiri a Jami'ar Cambridge tare da digiri na uku a fannin Archaeology a shekara ta 1994.[2]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Segobye ta yi aiki a matsayin Mataimakiyar Daraktar a Majalisar Binciken Kimiyyar Ɗan Adam ta Afirka ta Kudu. Daga nan ta yi aiki a Jami'ar Botswana kafin ta shiga aikinta na yanzu a matsayin shugabar Kimiyyar Ɗan Adam a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Namibia.[3] Ta kasance Shugabar Ƙungiyar Archaeological Association ta PanAfrican daga shekarun 2005 zuwa 2010.[4]

Karramawa[gyara sashe | gyara masomin]

Segobye zaɓaɓɓiya ce n'ta Kwalejin Kimiyya na Afirka (2018)[5] kuma farfesa mai daraja a Cibiyar Shugabancin Afirka ta Thabo Mbeki (TMALI), Jami'ar Afirka ta Kudu.[6] Tana aiki a hukumar haɗin gwiwar HIV/AIDS ta Afirka (ACHAP).[7]

An gayyace ta don yin jawabi na biyu na UNESCO Future Forum Africa a shekarar 2013.[1] Ta kasance malama mai ziyara a Bradford Rotary Peace Center (2016).[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "UNESCO Future Forum Africa #2: Decolonizing African Futures: Exploring and Realigning Alternative Systems" (PDF). UNESCO. 6 December 2013.
  2. Townsend, Leonie. "Prof Alinah Kelo Segobye". Welcome to Foresight For Development (in Turanci). Retrieved 2020-02-27.
  3. "Alinah Segobye | Faculty of Human Sciences". fhs.nust.na (in Turanci). Archived from the original on 2020-10-31. Retrieved 2020-02-27.
  4. "Congresses and Presidents – PanAfrican Archaeological Association". www.panafprehistory.org. Retrieved 2021-10-22.
  5. 5.0 5.1 "Segobye Alinah Kelo | The AAS". www.aasciences.africa. Archived from the original on 2020-02-27. Retrieved 2020-02-27.
  6. "Alinah Kelo Segobye". The Conversation (in Turanci). 25 May 2015. Retrieved 2020-02-27.
  7. "Welcome to ACHAP". www.achap.org. Archived from the original on 2020-02-10. Retrieved 2020-02-27.