Aliyu Shugaba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aliyu Shugaba
Rayuwa
Haihuwa 4 ga Afirilu, 1963 (60 shekaru)
Sana'a
Sana'a Malami

Aliyu Shugaba (An haife shi a shekara ta 1963) masani ne a Nijeriya, farfesa a fannin kimiyyar nazarin halittu wanda shi ne mataimakin shugaban jami’ar Maiduguri a jihar Borno, Nijeriya. Kafin nadin nasa ya kasance Mataimakin Mataimakin Shugaban Jami'ar akan ayyukan ilimi.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Aliyu Shugaba a shekara ta 1963 a kauyen Buratai na karamar hukumar Biu, jihar Borno. Shugaba ya fara karatun boko a makarantar firamare ta Buratai a shekarar 1970, bayan ya kammala a 1976 daga nan ya wuce makarantar Sakandaren Gwamnati ta Bama sannan ya kammala a 1981. Shugaba ya samu shiga Jami'ar Maiduguri a 1982 sannan ya ci gaba da samun karatun sa na B.Sc. Biochemistry a 1986. Shugaba ya kuma halarci Jami'ar Ahmadu Bello. Zaria inda ya sami M.Sc da PhD a Biochemistry tsakanin 1995 da 2005.[1][2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. University of Maiduguri Nigeria. "New VC Aliyu Shugaba". Archived from the original on 2021-01-20. Retrieved 2021-02-21.
  2. University of Maiduguri Nigeria. "Northeast Unimaid Gets New VC Aliyu Shugaba".