Jump to content

Aminu Dantata

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.


Aminu DantataAbout this soundAminu Dantata  ko kuma ace Aminu Alhassan Dantata, an haife shi a ranar 19 ga watan Mayu shekarar 1931, fitaccen dan kasuwa ne a Najeriya kuma mai taimakon jama'a, wanda ya tallafawa cibiyoyi daban-daban na inganta ilimi a Jihar Kano ta hanyar kirkirar shirye-shiryen koyar da sana'o'i ga jama'a.[1]

Shine shugaban da ke jagorantar dukkan harkokin kasuwancinsa na gidaje da sauran bangarorin shigar kudi.[2]

Dantata ne ya assasa kamfanin man fetur da iskar na na Express Petroleum & Gas Ltd kana daya daga cikin wadanda suka tsara Bankin Jaiz a Najeriya. A shekarar 1978, ya kasance mamban tafiyar siyasa ta National Movement wacce daga baya ta sauya zuwa National Party of Nigeria a turance.[3]

  1. Lucas, J. (1994). The State, Civil Society and Regional Elites: A Study of Three Associations in Kano, Nigeria. African Affairs, 93(370), 21–38. Retrieved from Jstor. Pp. 24–26
  2. http://peopleandpowerngr.com/2016/06/alhassan-dantatas-long-vibrant-legacy/
  3. Labinjoh, J. (1981). The National Party of Nigeria: A Study in the Social Origins of a Ruling Organization. Africa Spectrum, 16(2), 193–201. Pp. 194. Retrieved from Jstor.