Anatoliy Kokush
Anatoliy Kokush | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kerch (en) , 1951 (72/73 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | injiniya |
IMDb | nm4624648 |
Anatoliy Kokush ( Ukraine ; an haife shi a shekara ta 1951, Kerch, RSFSR ) injiniyan fina-finai ne na kasar Ukraine, ɗan kasuwa, kuma mai ƙirƙira. A shekara ta 2005, an ba shi lambobin yabo na Oscars guda biyu. Kyaututtukan sun kasance dangane da nau'in lambar yabo ta Kimiyya da Injiniyanci : an ba da guda ɗaya "don kirkir da haɓaka marikar na kyamarar Arm gyro-stabilized na Rasha da kuma Kan Jirgi"; an kuma bashi ɗayan lambar yabon ne "don kirkira da haɓaka jerin cranes na hotuna masu motsi na Cascade". [1] Uwargidan shugaban kasar Ukraine Kateryna Yushchenko ita ta jinjina wa Kokush saboda gudunmawar da ya bayar ga sinimar Yukren da ma duniya baki daya. [2]
Kokush ya kammala karatunsa daga Cibiyar Injiniyanci ta Leningrad a 1974. Daga nan ya fara aiki da Dovzhenko Film Studios a Kyiv.[3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Academy Awards 2006 – IMDb
- ↑ Oscar-winning cinematographer revolutionizes film industry Article from Kyiv Post
- ↑ "The International Kyiv Film Festival nominee page 2007 Archived 26 July 2013 at the Wayback Machine (in Ukraine)
Hanyoyin haɗi na waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Gidan yanar gizon Filmotechnic na hukuma
- "Кокуш U.Crane" Archived 2019-10-23 at the Wayback Machine (a cikin Ukrainian)