Angue Ondo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Purificación Angue Ondo jami'ar diflomasiyya ce daga Equatorial Guinea, kuma jakadar kasa a Amurka. Ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta matsayin mata aciki da wajen iyakokin kasarta.

Sana'arta[gyara sashe | gyara masomin]

Angue Ondo ta sami horo amatsayin malama kuma ta fara aiki amatsayin malama a shekara ta 1964. A shekara ta 1968, ta bar koyarwa kuma tana aiki a Ma'aikatar Harkokin Waje, lokacin da aka kama ta, wanda shi ne na farko na kama da yawa acikin shekaru biyar masu zuwa, saboda dalilan da ba tada tabbas. [1]

A karkashin Shugaba Francisco Macías Nguema, an tsare ta a lokuta da dama, kuma daga karshe ta gudu zuwa Gabon makwabciyarta,inda tayi zaman gudun hijira daga shekarar 1973 zuwa shekara ta 1980, tana koyar da Mutanen Espanya a wata makaranta a can.

A shekara ta 1981, an nadata a matsayin mataimakiyar Ministar Kwadago, Tsaron zamantakewa da inganta mata. A cikin shekarun 1990, Angue Onde tayi aiki a ma'aikatar bunkasa mata ta Equatorial Guinea kafin ta zama jakada a Kamaru kuma tun shekara ta 2005 ta zama jakada a Amurka.

Rayuwarta ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Angue Ondo uwa ce daya tilo kuma uwar yara shida.

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named elpais