Antonieta Rosa Gomes

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Antonieta Rosa Gomes (an haife ta a ranar 4 ga watan Mayu, 1959, a Bissau) 'yar siyasar Bissau-Guinean ce.

Wacce ta kafa kuma shugabar kungiyar Guinean Civic Forum–Social Democracy, Gomes ta yi karatu a Brazil, ta sami digirinta na shari'a daga Jami'ar São Paulo. Ta yi aiki a ƙarƙashin Kumba Ialá a matsayin ministar shari'a da kuma ministar harkokin waje a wurare daban-daban. Ta tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasa na shekarun 1994, 1999, da 2005. Ita ce mace ta farko da ta yi haka, amma ba ta taɓa samun fiye da kashi 2% na kuri’un da aka kaɗa ba.[1] Ana dai kallon korar ta a matsayin ministar harkokin wajen ƙasar a matsayin babban abin da ya haifar da juyin mulkin shekarar 2003 wanda ya hambarar da Ialá daga kan ƙaragar mulki. A cikin shekarar 2004, ta yi aiki a matsayin shugabar hukumar Kotun Koli ta Shari'a.[2] Ta tsaya takarar shugaban ƙasa a shekarar 2005 akan tikitin FCG tare da alaƙa da Social Democracy. Ita kaɗai ce mace a zaɓen. Fórum Cívico Guineense-Social Democracia ta daina fitowa a zaɓen 'yan majalisa a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2008, da ranar 13 ga watan Afrilu, 2014. Ta kuma dena sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa a ranar 28 ga watan Yuni, 2009, 18 ga watan Maris, 2012, da ranar 13 ga watan Afrilu, 2014.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Peter Karibe Mendy; Lobban Jr. (17 October 2013). Historical Dictionary of the Republic of Guinea-Bissau. Scarecrow Press. ISBN 978-0-8108-8027-6.
  2. Kathleen E. Sheldon (2005). Historical Dictionary of Women in Sub-Saharan Africa. Scarecrow Press. ISBN 978-0-8108-5331-7.