Jump to content

Audu Kano Karkuzu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Audu Kano (Karkuzu) Tsohon jarumi ne a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood ya Dade Yana fim a masana'antar yayi Fina finai da dama a masana'antar, Ya fito a shahararren tsohon fim din Nan Mai suna "Bilkisu Mai gadon zinare" tare da jarumi [[Ibrahim m}Maishinku]] da Kuma jaruma Jamila Nagudu, ya kuma fito a gawurtaccen fim mai suna wuta da Aljan. Ya kwashe shekaru 33 a masana'antar

Takaitaccen Tarihin Sa

[gyara sashe | gyara masomin]

Audu Kano cikakken sunan sa shine Abdullahi Shu'aibu anfi sanin sa da "karkuzu na bodara " ko Kuma Audu kano, a yanzun haka Yana zaune a garin Jos, ya tsufa a halin yanzu inda a kwanakin baya aka nuna bidiyon sa na cewa beda lafiya ya makance. Inda aka tallafa masa.

Sunan Karkuzu

[gyara sashe | gyara masomin]

An fi saninsa da sunan Audu Karkuzu, ya sami sunan Karkuzu ne ta wani take da ake masa ko kirari "Karkuzu na bodara iKon Allah na bodara malam" kafin ya shigo masana'antar fim ,ya kasance Dan tireda ne Mai kasa kaya ko a baro ko a benci suna seda irin su agogo da gilas. Sai suka haɗa sani kwamiti na wasan kwaikwayo, sun fara wasan a fili har zuwa kan titin daga Nan har Allah ya Kai su gidan talabijin na NTA Jos a lokacin shekara hudu da bude gidan talabijin din.[1]

  1. https://aminiya.ng/yadda-na-samu-sunan-karkuzu-na-bodara-audu-kano/