Auwal Musa Rafsanjani
Auwal Musa Rafsanjani ɗan gwagwarmayar kare hakkin dan adam ne a kasar Najeriya, kuma Babban Darakta na Cibiyar Ba da Shawara ta Jama'a . [1][2] Bugu da kari, Shi ne shugaban Kwamitin Amnesty International, na Najeriya . [3]
Rayuwa ta farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Rafsanjani a garin Kano kuma ya sami digiri na farko a kimiyyar siyasa a Jami'ar Bayero Kano . [4][5] A shekara ta alif dubu daya da casa'in da biyu (1992), ya zama Mataimakin Sakatare Janar na Ƙungiyar Daliban Najeriya (NANS). [6]
Ya yi aure a shekara ta dubu biyu da daya (2001) kuma ya haifi ɗansa na farko a shekara ta dubu biyu da uku (2003).[7]
Gudanarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Rafsanjani ya kasance dan kungiya na Ƙungiyar 'Yancin Bil'adama kuma dan kungiya na Cibiyar Dimokuradiyya da 'Yancin Dan Adam . [8] Ya kasance dan kungiya na kafa yaki don Dimokuradiyya, wanda marigayi Beko Ransome Kuti, Democratic Alternative, yakasance jagora kuma dan kungiya, kuma mai kula da kungiyar United Action for Democracy (UAD) wanda Olisa Agbakoba ta jagoranta.[9]
A shekara ta dubu biyu da biyar (2005), ya kafa Cibiyar Gudanar da Shari'a ta Jama'a (CISLAC), wacce kungiya ce mai zaman kanta, kuma ba kungiyar neman riba bace tare da sanya muhimmin aikin ta ya zama inganta mulkin demokraɗiyya da zurfafa dimokuradiyya ta hanyar bayar da shawarwari, gina iyawa, bincike, da raba bayanai.[10][11][12]
Sannan kuma, shi mai sharhi ne a fili, wato ba sirri ba na jaridu, shirye-shiryen Rediyo da Talabijin: Al-Jazeera, CNN, BBC, NTA, AIT, TVC, Channel TV, VOA, Rediyon Jamus, Rediyo Faransa da Rediyo Iran, FRCN, da sauransu a cikin yarukan Hausa da turanci.[13][14][15][16][12]
Baya ga gabatar da takardu da yakeyi a abubuwan da suka faru na kasa da kasa, Auwal Musa ya rubuta takardu da dama wadanda suka samu aka buga su a duk faɗin jaridu na kasashe da mujallu na kasa da kasa.
Ya kasance kuma yana ba da shawara gameda mata da yara mata waɗanda aka tilasta musu yin aikin wahala cewa ya kamata a sami manufofi da tsare-tsare da za a iya amfani da su don magance matsalar da kuma samar da tsararrun ayyuka da aminci a gare su.[17][18]
Auwal Musa ya kasance mai wakili a Taron Kasa wadda ya gudana a kasar Najeriya 2014 wakiltar Ƙungiyoyin Jama'a.[19]
An kuma nada shi a matsayin shugaba na kungiyar Kula da Canje-canje a shekarar 2021.[20]
Bayanan da aka ambata
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ DailyNigerian (2022-08-19). "INTERVIEW: I'm no match for Keyamo, my activism dates back to 1989 – Rafsanjani". Daily Nigerian (in Turanci). Retrieved 2023-08-06.
- ↑ "TMG elects Rafsanjani as new chair - Daily Trust". dailytrust.com. Retrieved 2023-08-10.
- ↑ Ewepu, Gabriel (8 August 2019). "Amnesty Chair dares protesters, says no intimidation can stop us". Vanguard News. Retrieved 10 August 2023.
- ↑ Kasali, Segun (May 15, 2022). "How I got my nicknames Rafsanjani". Tribune Online (in Turanci). Archived from the original on March 29, 2024. Retrieved 2024-03-29.
- ↑ "AUWAL MUSA RAFSANJANI - THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Retrieved 2024-03-28.
- ↑ "Auwal Rafsanjani: I grew up fighting for poor people". The Nation Newspaper. 5 May 2019. Retrieved 10 August 2023.
- ↑ George, Godfrey (2023-11-17). "My marriage...With Auwal Musa (Rafsanjani)". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-03-29.
- ↑ "Why I am committed to activism and humanity".
- ↑ Nigeria, Guardian (2018-05-26). "'Why I am committed to activism and humanity'". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Retrieved 2023-08-06.
- ↑ "How I got my nicknames —Rafsanjani". Tribune Online (in Turanci). 2022-05-15. Retrieved 2023-08-06.
- ↑ "Why NASS attrition rate is rising – CISLAC - Daily Trust". dailytrust.com (in Turanci). 2018-04-21. Retrieved 2024-03-29.
- ↑ 12.0 12.1 "Matsalar Cin Hanci Da Rashawa Ba Ta Sauya Ba A Najeriya - Rahoto". Voice of America. 2022-01-26. Retrieved 2024-03-29. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ DailyNigerian (2022-08-19). "INTERVIEW: I'm no match for Keyamo, my activism dates back to 1989 – Rafsanjani". Daily Nigerian (in Turanci). Retrieved 2024-03-29.
- ↑ Nigeria, Guardian (2018-05-26). "'Why I am committed to activism and humanity'". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Retrieved 2024-03-29.
- ↑ Uwimana, Auwal Musa Rafsanjani,Chantal. "Fighting corruption in Nigeria requires action not words". Al Jazeera (in Turanci). Retrieved 2024-03-29.
- ↑ "Auwal Musa Rafsanjani | Al Jazeera News | Today's latest from Al Jazeera". Al Jazeera (in Turanci). Retrieved 2024-03-29.
- ↑ "Auwal Rafsanjani - THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com (in Turanci). Retrieved 2024-03-29.
- ↑ "Waiting for the Cavalry… 365 Days". Fiction & Development (in Turanci). 2015-04-14. Retrieved 2024-03-29.
- ↑ "President Jonathan Releases Final List Of Delegates To The National Conference | Sahara Reporters". saharareporters.com. Retrieved 2024-03-28.
- ↑ Abdulsalam, kabir (2021-08-27). "Auwal Rafsanjani Elected Chairman Transition Monitoring Group". PRNigeria News (in Turanci). Retrieved 2024-03-28.