Azonto Ghost

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Azonto Ghost
Asali
Lokacin bugawa 2013
Asalin harshe Yaren Akan
Ƙasar asali Ghana
Characteristics
Genre (en) Fassara thriller film (en) Fassara

Azonto Ghost fim ne na ƙasar Ghana wanda ke nuna Liwin a matsayin babban jarumi. A cikin fim ɗin 'yan uwansa ne suka kashe shi, saboda mahaifinsu ya bar masa kaso mai tarin yawa na gadonsa. Fatalwarsa ta yi farautarsu ta kashe su ɗaya bayan ɗaya. Lokacin da yake raye yana son rawar Azonto. Don haka duk lokacin da ya kai hari kan wani ɗan uwansa sai ya fara rawa.[1][2]

'Yan wasa[gyara sashe | gyara masomin]

  • Kwadwo Nkansah (Liwin)
  • Bill Asamoah
  • Patricia Bentum
  • Benedicta Ghafa

A cikin shahararrun al'adu[gyara sashe | gyara masomin]

Wannan fim ɗin ya zama wahayi zuwa ga wani shahararren meme inda mahaifin Liwin ya ce "Oh my God! Wow!" ta hanyar farin ciki.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Broohm, Beverly. "Azonto Ghost' was my breakthrough song - Bisa Kdei". Myjoyoline. Beverly Broohm. Retrieved 14 November 2018.
  2. "Azonto Ghost Reloaded With Lil Wayne". Modern Ghana (in Turanci). 2013-02-21. Retrieved 2018-11-14.
  3. "This is Where the 'Oh My God, Wow' Meme Comes from". 13 March 2018.