Bakan gizo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Bakan gizo
subclass ofphotometeor Gyara
Unicode character🌈 Gyara
Bakan gizo
Bakan gizo

Bakan gizo wani muhimmin haske ne da yake bayyana a cikin giza gizai a sararin samaniya wanda zakaga yayi lankwasa kamar misalin baka ya dangana daga kusurwa zuwa kusurwa. A turance ana kiransa Rainbow. Shi dai wannan abu yana dauke da kaloli daban-daban har kusan guda bakwai, mafi akasari yana bayyana ne lokacin da hadari ya taso, cikin ikon Allah da zarar bakan gizo ya bayyana, nan take zakaga hadarin ya lafa ma'ana zai washe zuwa wani dan lokaci daga nan kuma sai Ruwa ya kece. Amma mafi akasari wani lokacin sam baza ma ayi ruwan ba.

Wannan dalilin ne yasa Hausawa tun kaka da kakanni suke bayyana shi a matsayin cewa shi bakan gizo wai yana fitowa ne daga tsohuwar rijiya domin ya shanye ruwan dake cikin giza gizai, da zarar ya sha ya koshi to sai ya amayar da ruwan daya sha, shine zai zubo a matsayin ruwan sama.

Wannan dai tun kaka da kakanni haka ake cewa kafin masana ilimin kimiyya su shiga lamarin.

BAKAR GIZO A KIMIYYANCE[gyara sashe | Gyara masomin]

Masana ilimin kimiyya na duniya sunyi ruwa sunyi tsaki domin binciko menene hakikanin bakar gizo, kuma daga ina yake, kuma me yasa yake bayyana, kuma ta yaya yake bayyana.

Binciken masana ilimin kimiyya dai ya tabbatar da cewa bakan gizo wani haske ne da yake bayyana a sararin samaniya a wasu lokuta idan hasken rana ya ratsa ta cikin giza gizai masu dauke da feshin ruwa.

Tabbas wannan zance na ƴan kimiyya yafi kamshin gaskiya a bisa kwarara hujjoji da kuma na'urori na musamman dan bincike.

GWAJI CIKIN SAUKI[gyara sashe | Gyara masomin]

Idan kana so ka gwada fitar da bakar gizo zaka iya da kanka ba tare da amfani da na'ura ba:

1.Abu na farko da zaka tanada shine ruwa sai ka gumtsa a bakinka sai ka fita cikin hasken rana sai ka fesa ruwan, kana fesawa kana kallon cikin feshin nan take zakaga launuka daban-daban sun bayyana.

2.Ko kuma kasami madubi sai kaba abokinka ko wani ya tsaya a haske rana sai ya walwala hasken dake cikin madubin zuwa cikin daki kodai wani lungu mai dan duhu sai ka fesa ruwa acikin hasken nan take zaka kaloli sun bayyana har da lankwasa kamar dai misalin yadda yake bayyana a sama.

IRE-IREN BAKAN GIZO[gyara sashe | Gyara masomin]

1.Wani lokaci guda daya ne yake bayyana wato gwauro bakan gizo kenan kamar yadda wasu ke cewa.

Nau,oin Bakan gizo

2.A wani lokacin kuma guda biyu ne suke bayyana a lokaci daya, irin wadannan su wasu kewa lakabi da tagwaye.

Anazarci[gyara sashe | Gyara masomin]