Balle, Najeriya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Balle, Najeriya

Wuri
Map
 13°28′N 4°40′E / 13.47°N 4.67°E / 13.47; 4.67
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihajihar Sokoto
Ƙaramar hukuma a NijeriyaGudu
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Balle gari ne, da ke a jihar Sokoto, a Najeriya. Kuma garin ne Hedikwatar karamar hukumar Gudu.

Balle na da tazarar kilomita 36 daga garin Tangaza, da kuma kimanin kilomita 97 daga Sakkwato.

Yanki[gyara sashe | gyara masomin]

Balle na a gabashin Gudu, kimanin kilomita 40 kudu maso gabas da garin Kurdula, kuma garin Karfen-Sarki yana da nisan kilomita 30 kudu maso yamma, garin Bachaka kimanin kilomita 70 daga yamma. Kasancewar ita ce hedkwatar karamar hukumar Gudu da yawa gine-ginen jama'a da na gwamnati suna cikin garin. Kamar Sakatariyar Kananan Hukumomi, Gidan Gwamna, Gidan Ma'aikata da dai sauransu.

Makarantu[gyara sashe | gyara masomin]

Garin balle, yana da makarantun firamare na kwana guda uku mallaki gwamnatin jihar Sokoto, da kuma sabuwar makarantar sakandare da aka gina, ƙaramar sakandare da Model Primary School Balle.

Harshe da Ƙabila[gyara sashe | gyara masomin]

Mazaunan Balle sun haɗa da Hausawa da kuma Fulani, galibi ana amfani da harshen Hausa, haka nan kuma ga yaren fulbe ga wasu mazauna yankin.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]