Bao Fan
Bao Fan | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1970 (53/54 shekaru) |
ƙasa | Sin |
Mazauni | Shanghai |
Karatu | |
Makaranta |
Fudan University (en) BI Norwegian Business School (en) |
Harsuna |
Standard Chinese (en) Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | Ma'aikacin banki da investor (en) |
Employers |
Credit Suisse (en) China Renaissance (en) Morgan Stanley (mul) AsiaInfo (en) |
Bao Fan ( Chinese ; An haife shi a shekara ta 1970) ma'aikacin bankin zuba jari ne na kasar Sin, kuma shugaban kamfanin Chaina Renaissance na kasar Sin, kamfanin da ya kafa a shekara ta 2005.
A cikin 2015,( Bloomberg Markets) ta saka Bao akan a matsayin na 22 cikin jerin mutane 50 Mafi Tasiri.[1]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Bao a Shanghai ga iyayen da suka yi aiki a gwamnati. Dangane da matsayin iyayensa a cikin gwamnati, Bao ya lura cewa ba wani abu bane babba, ni ba daya daga cikin yarima ba.[2] Ya yi makarantar sakandare a Amurka.
Ya sami digiri daga Jami'ar Fudan ta Shanghai da Norwegian School of Management.[3]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Bao ya sake yi wa Morgan Stanley, Credit Suisse da Morgan Stanley aiki a London, New York da Hong Kong. A shekara ta 2000, Bao ya bar Morgan Stanley ya zama babban jami'in tsare-tsare a farawar sa aiki a ChinaInfo Holdings.[4][5]
A shekara ta 2005, Bao ya kafa kasar Chaina Renaissance, wata babbar cibiyar hada-hadar kudi ta kasar Sin da aka sadaukar da ita ga sabbin kasuwancin tattalin arzikin kasar Sin. Kamfanin ya fara aiki a matsayin kamfanin ba da shawara kan harkokin kudi, babban aikin Renaissance na kasar Sin a yanzu ya kunshi hada-hadar bankin zuba jari, sarrafa zuba jari da sarrafa dukiya.[ana buƙatar hujja]
Ya zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2020, Chaina Renaissance ya ba da shawara akan cinikayya/kasuwancin da ya gudana kusan 980 da darajar kudin kididdigar kasuwancin ta kai dala biliyan 146 tun daga lokacin da aka kafa kamfanin, kuma asusun kamfanoni masu zaman kansu na da AUM kusan RMB39.0 biliyan a sabbin jarin tattalin arziki.[ana buƙatar hujja]
China Renaissance Holdings Limited ana jera su akan Babban Hukumar HKEX a cikin 2018, a ƙarƙashin hannun jari (1911. HK).[ana buƙatar hujja]
Tun a shekara ta 2013, kamfanin ya fara gudanar da harkokin zuba jari mai zaman kansa. Bao shi ne abokin kafa kuma babban jami'in zuba jari na kasuwancin kula da zuba jari na kamfanin. Huxing Capital Growth Capital, alamar zuba jari na Chaina Renaissance ya zuba jari a cikin sabbin 'yan kasuwa na tattalin arziki da kamfanoni na gida sama da 100, kuma ya taimaka sama da 30 daga cikin wadannan kamfanoni shiga bainar jama'a a kasar Sin da kasuwannin duniya. Kuɗaɗen sa na sirri sun ƙididdige matsakaicin babban jari (MOIC) na 2.5x da ƙimar dawowa (IRR) na kashi 33 cikin ɗari kamar na 30 ga watan Yuni 2020. Kamfanonin, portfolio companies of Huaxing Growth Capital, sun hada da Pop Mart, Kuaishou, Beike Zhaofang ( Lianjia ), Jiangxiaobai, Didi Chuxing, Meituan, Li Auto, WuXi AppTec, MININGLAMP Technology, Focus Media, LEXIN da Micro-Tech Endoscopy.[6]
A watan Fabrairun 2016, Chaina Renaissance na kasar ya sami lambar yabo ta FinanceAsia Achievement Awards a mastsayin gwarzon "Best China Deal" da "Best Private Equity Dea".[7] "Best China Deal" hakan ya biyo baya, laakari da rawar da kamfanin ya taka a matsayin mai ba da shawara a kan kudi don "haɗin gwiwar dabarun" Meituan da Dianping. [7] Meituan-Dianping shi ne gidan yanar gizo mafi girma na rukunin jerin gidajen yanar gizo na China, kuma a cikin watan Janairu 2016 ya samu dala biliyan 3.3, yana kimanta kamfanin da aka hade akan dala biliyan 18. Kamfanin ya yi iƙirarin cewa wannan shi ne mafi girma na bayar da kuɗi na China don fara Intanet mai samun goyon bayan kasuwanci.[8]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Bao yana zaune a birnin Beijing.[6]
Bacewa
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Fabrairun 2023, BBC da wasu majiyoyi sun ba da rahoton cewa Bao ya bace tsawon kwanaki biyu kuma ba su san inda yake ba.[9][10][11] Bacewar ta sa, ta sa hannun jarin kamfanin na Chaina Rennesaence na kasar Sin ya ragu da kashi 50 cikin 100,[12] ko da yake, kamfanin ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewa "Ayyukan za su ci gaba bisa ka'ida".[13]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Fan Bao". Bloomberg. 5 Oct 2015. Retrieved 20 February 2023.
- ↑ "Upstart Bank in China Rides High on Technology I.P.O. Crest". The New York Times. Retrieved 2 February 2016.
- ↑ "Fan Bao - Biography". 4-traders.com. Retrieved 2 February 2016.
- ↑ "Mr. Fan Bao, interviewed by China Daily_China Renaissance". Huaxing.com. Retrieved 2 February 2016.[permanent dead link]
- ↑ "Fan Bao". LinkedIn. Retrieved 2 February 2016.
- ↑ 6.0 6.1 William Mellor (11 May 2015). "Chinese Investment Banker Fan Bao Searches for Next Jack Ma - Bloomberg Business". Bloomberg.com. Retrieved 2 February 2016.
- ↑ 7.0 7.1 "China Renaissance Wins "Best China Deal" and "Best Private Equity Deal" in FinanceAsia's Achievement Awards 2015 - Yahoo Finance". Finance.yahoo.com. Retrieved 2 February 2016.
- ↑ "Meituan-Dianping, China's Largest Group Deals Site, Closes Massive $3.3B Round At $18B Valuation". TechCrunch. 20 January 2016. Retrieved 2 February 2016.
- ↑ https://www.bbc.com/hausa/articles/c1wjj1g0l38o
- ↑ Joel Guinto; Fan Wang; Frances Mao (17 February 2023). "Bao Fan: Billionaire tech banker in China reported missing". BBC News.
- ↑ https://www.aninews.in/news/world/asia/chinas-billionaire-ceo-bao-fan-disappears-share-stock-plunges20230220032116
- ↑ https://www.aninews.in/news/world/asia/chinas-billionaire-ceo-bao-fan-disappears-share-stock-plunges20230220032116
- ↑ https://www.aninews.in/news/world/asia/chinas-billionaire-ceo-bao-fan-disappears-share-stock-plunges20230220032116
- All articles with dead external links
- Articles with dead external links from December 2019
- Articles with invalid date parameter in template
- Articles with permanently dead external links
- All articles with unsourced statements
- Articles with unsourced statements from November 2022
- Haifaffun 1970
- Rayayyun mutane