Bassirou Diomaye Faye
Bassirou Diomaye Faye | |||
---|---|---|---|
2 ga Afirilu, 2024 - ← Macky Sall (mul) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | N’Diaganiao (en) , 25 ga Maris, 1980 (44 shekaru) | ||
ƙasa | Senegal | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama |
Marie Khone Faye (en) Absa Faye (en) (4 ga Faburairu, 2023 - | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Université Cheikh Anta Diop (en) National School of Administration of Senegal (en) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | tax inspector (en) da ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci | ||
Jam'iyar siyasa | African Patriots of Senegal for Work, Ethics and Fraternity (en) |
Bassirou Diomaye Faye, (an haife shi a ranar 25 ga watan Maris shekara ta 1980), shine shugaban Senegal na biyar kuma tsohon mai duba haraji.[1] Shi ne tsohon babban sakataren rusasshiyar ƙungiyar PASTEF kuma ya tsaya takara a madadin Ousmane Sonko wanda rashin cancantar shine ya sa aka hana shi takara. shine shugaban Senegal na biyar kuma tsohon mai karɓar haraji.
Ilimi da farkon aiki
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin shekarar 2000, Faye ya sami digirinsa na baccalaureate. Yayi nasarar samun digirin digirgir a fannin shari’a, daga nan kuma yayi nasarar kammala jarrabawa biyu na gasa, inda ya shiga makarantar kula da harkokin mulki ta ƙasa (ENA) da kuma majistire a shekarar 2004. Bayan kammala karatunsa, ya zaɓi zama mai duba haraji a sashen haraji da kayyade, inda ya zama babban jami’in kula da haraji a bangaren haraji da gidaje. sun yi abota da Sonko wanda sun haɗu ne a makaranta.
Dangantakar Faye da Sonkos ta ƙara ƙarfi ne a shekarar 2014, a cikin ƙungiyar Haraji da Kayayyaki, wanda Sonko, shugaban sabuwar ƙungiyar PASTEF ya ƙirƙira. A lokacin da yake shugaban ƙungiyar, Faye yayi kamfen don sauƙaƙa mallakar gidaje ga masu biyan haraji da kadarori.
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Da farko baƙo ne a lokacin da aka kafa jam’iyyar, Faye ya yi gaggawar hawa har ya zama daya daga cikin fitattun mutane a cikin jam’iyyar. Ya cigaba da zama ɗaya daga cikin masu aƙida kuma masu tsara shirin Sonko na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019. Sonko ya samu kusan kashi 16% na ƙuri’un da aka kaɗa kuma ya zo na uku.
A watan Fabrairun shekarar 2021, Faye ya zama babban sakatare na PASTEF bayan an kama Sonko, ana tuhumarsa da laifin fyaɗe da ma’aikacin ɗakin tausa ya yi. A wani ɓangare na dabarunsa na samun mulki, Faye ya yi yunƙurin haɗa kan ƴan adawa don zaɓen 2022, inda ya lashe kujeru 56 a ƙarƙashin kawancen ƴantar da Jama'a.
Dauri da saki
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 14 ga Afrilu, shekarar 2023, an kama Faye yayin da yake fitowa daga ofishin haraji da ƙaddara a Rue de Thiong a Dakar. Bayan haka, an miƙashi a hannun ƴan sanda bisa tuhumarsa da akeyi akan " yaɗa labaran karya, wulakanta kotu, da kuma ɓata sunan hukumar da aka kafa" biyo bayan wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumunta. A cikin wannan saƙon, ya yi tir da rashin adalcin da ake gani a cikin tsarin shari'a, inda ya hango hukuncin da ka iya haramtawa Sonko shiga takaddamar shari'a tsakanin PASTEF da ministan yawon buɗe ido, Mame Mbaye Niang. A yayin da al’amarin ya ci gaba, an ƙara gabatar da wasu tuhume-tuhume da suka haɗa da tada ƙayar baya da kuma tauye tsaron ƙasa a kansa, wanda ya haifar da tsare shi na tsawon lokaci.
Bayan yunƙurin da shugaba mai ci Macky Sall ya yi a watan Fabrairu na ɗage zaɓen saboda rashin warware taƙaddama kan wanda zai iya tsayawa takara, an yi zanga-zanga da yawa tare da majalisar tsarin mulkin ƙasar ta soke dage zaben.[2] Dangane da zanga-zangar da kuma kifar da gwamnatin Sall ya ce zai bar ofis kamar yadda aka tsara ranar 2 ga Afrilu, inda ya sanya ranar 24 ga Maris.[3] Ya kuma bayyana aniyar sa na sakin Sonko, Faye da dukkan magoya bayansu a matsayin aiki na kwarai.[4] A ƙarshen watan Fabrairu, gwamnati ta gabatar da ƙudirin yin afuwa don kwantar da hankulan zamantakewa da siyasa.[5] Gwamnati ta saki fursunonin siyasa da yawa,[6] kuma a ranar 14 ga Maris, kwanaki kafin zaɓen, an saki Sonko da Faye daga kurkuku.[7]
Iyalai
[gyara sashe | gyara masomin]Faye yanada mata biyu; Marie Khon Faye da Absa Faye. Marie Khon, ƴar uwan mijinta, sun haifi ƴa-ƴa huɗu, maza 3 da mace guda. Bai haihu da Absa ba.[8] Faye da Sonko abokai ne na kut-da-kut, har ma ya sanya wa ɗayan sunayen 'ya'yansa Ousmane don girmama abokantakarsu.[9]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://apanews.net/bassirou-diomaye-faye-what-is-senegals-opposition-contender-about/
- ↑ https://www.bbc.com/news/world-africa-68326782
- ↑ https://www.bbc.com/news/world-africa-68497489
- ↑ https://www.bbc.com/news/world-africa-68379420
- ↑ https://en.wikipedia.org/wiki/Bassirou_Diomaye_Faye#cite_note-10
- ↑ https://www.france24.com/en/tv-shows/eye-on-africa/20240222-senegal-justice-ministry-says-over-300-prisoners-released-in-a-week
- ↑ https://www.bbc.com/news/world-africa-68562465
- ↑ https://www.xalimasn.com/en-route-vers-le-palais-voici-les-femmes-de-bassirou-diomaye-faye/
- ↑ Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs named:0