Jump to content

Booker T (Dan dambe)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Booker T (wrestler))
Booker T (Dan dambe)
Rayuwa
Cikakken suna Robert Booker Tio Huffman
Haihuwa Houston, 1 ga Maris, 1965 (59 shekaru)
ƙasa Tarayyar Amurka
Ƴan uwa
Abokiyar zama Sharmell Sullivan-Huffman (en) Fassara  (ga Faburairu, 2005 -
Ahali Lash Huffman (en) Fassara
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a professional wrestler (en) Fassara
Nauyi 116 kg
Tsayi 191 cm
Employers WWE SmackDown (en) Fassara
Muhimman ayyuka WWE Superstars (en) Fassara
Kyaututtuka
Sunan mahaifi Black Snow, Booker, Booker T, GI Bro, King Booker da Kole
IMDb nm0400259
Booker T

Robert Booker Tio Huffman Jr. (an haife shi ne a ranar 1 ga watan Maris, 1965) wanda aka fi sani da sunansa na dandali Booker T, Ba'amurke ne ƙwararren ɗan wasan kokawa, mai tallata ƙwararrun masu kokawa, masanin launi kuma mai sharhi kan launuka. Yana daga jerin 'yan wasan dambe na WWE, kuma shi ne wanda ya kafa kamfanin independent promotion Reality of Wrestling (ROW) a Texas City, Texas. Abokai da masu sharhi na masana'antu sun sanya Booker a matsayin ɗaya daga fitattun ƙwararrun masu kokawa a zamaninsa; a shekarar 2013 ya taba lashe kambun World's Heavyweight Champion na WWE.

Booker T

Huffman shi ne ƙarami a cikin yara takwas ɗin da iyayen sa suka haifa a Plain Dealing, Louisiana, kodayake an samu rarrabuwar ruwaya kan asalin mahaifars cewa haifaffen Houston, ne a Texas. A lokacin da Booker yake da shekaru 13, iyayensa biyu duk suka mutu kuma ya rayu tare da yayarsa mai shekaru 16. Babban wansa Lash "Stevie Ray" shi ne abokin tafiyarsa zuwa makarantar sakandare lokacin Huffman yana ɗan shekara 17. A cikin makarantar sakandaren, Huffman ya kasance ɗan kiɗan goge. Yana kuma buga kwallon kafa da kwallon kwando.