Jump to content

Bristan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Bristan sanannen nau'in kayan famfo ne a Ƙasar Ingila, galibi ana samun su a cikin kayan wanka. Har ila yau, sunan kamfanin iyaye ne, Bristan Group .

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

An kafa kamfanin ne a cikin shekara ta 1977 da mutane biyu tare da sunayen farko Brian da Stan, an hada sunayen biyu don samar da Bristan.[1] Ya fara ne ta hanyar sayar da kan famfona da famfon wanka zuwa DIY chain, galibi yanzu tsohuwar Texas Homecare. Yana ikirarin cewa shine kamfani sabo wanda yake gera famfonan bayi da na wanka a Ingila.

A shekara ta 1997 yana da gudanarwa na cini kayya (MBO). A shekara ta 2004 Masco mai hedikwatar Amurka ce ta sayi shi, wanda ya haɗa shi da wasu kamfanoni don kafa Bristan Group.

Wurin da yake[gyara sashe | gyara masomin]

Bristan Group shine ma mallakin Heritage Bathrooms. Dukansu Bristan da Heritage Bathrooms suna kan Birch Coppice Business Park a Dordon a Arewacin Warwickshire, a kan A5 (Watling Street), da mil a gabashin mahaɗar 10 (Tamworth) na M42. Yankin kudancin masana'antu yana cikin Baddesley Ensor, kuma duk shafin shine tsohon Baddesley Colliery, tare da layin dogo mai kusanci wanda yake nan haryanzu.

Kamfanin iyaye na Bristan Group shine Masco, wanda ke da hedikwata a Taylor, Michigan.

Shugabanni[gyara sashe | gyara masomin]

Babban Darakta na Bristan Group shine Jeremy Ling, wanda aka nada shi a watan Agustan shekara ta 2009.[2] Shugaba kuma tsohon Babban Darakta har zuwa 2008, Steve Lee, ya bar aiki a watan Yunin 2010.

Kayayyaki[gyara sashe | gyara masomin]

  • Famfona
  • Famfon wanka

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Company history". Archived from the original on 2016-05-04. Retrieved 2019-06-15.
  2. "Builders Merchants journal". Archived from the original on 2015-04-02. Retrieved 2015-03-04.

Haɗin waje[gyara sashe | gyara masomin]