Broken Mirror (fim)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Broken Mirror (fim)
Asali
Lokacin bugawa 2014
Asalin suna Broken Mirror
Asalin harshe Turanci
Ƙasar asali Ghana
Characteristics
Genre (en) Fassara drama film (en) Fassara
Direction and screenplay
Darekta Mikki Osei Berko
'yan wasa

Broken Mirror fim ne na ƙasar Ghana wanda aka saki a Shekara ta 2014 ta hannun kamfanin Media 5 Studio Productions. James Gardiner, Fred Amugi, Jackie Appiah, Roselyn Ngissah, Mikki Osei Berko, Victoria Lebene Mekpah da Jasmine Baroudi su ne taurarin da suka taka rawa a wasan. Pappa Deric ne ya rubuta, kuma David Owusu ne ya shirya shi tare da Mikki Osei Berko a matsayin darakta. Labari ne na wata mata da ta yi ta dirar mikiya lokacin da dukiyar saurayinta ta canza, bayan ta tsaya masa a cikin mawuyacin hali.[1]

Makirci[gyara sashe | gyara masomin]

Thompson wanda James Gardiner ya fito a matsayin a cikin shirin, ya kammala karatun jami'a haka-zalika baida aikin yi wanda ya rungumi aikin kafinta a matsayin wani yunƙuri don tsira da mutuncinsa. Mai ƙaunarsa Priscilla ( Jakie Appiah ) ya ba shi goyon baya har da na kuɗi. Priscilla wacce ba ta da arziki kuma tana aiki a matsayin mai dinki, abokan aikinta Evelyn (Roselyn Ngissah) da Angela (Victoria Lebene Mekpah) koyaushe suna yiwa Thompson abin bacin rai saboda kauna da goyon bayanta ga Thompson. Bangaskiyarta game da samun nasara a lokacin ibada yana da ƙarfi sosai kuma yana yi a cikin shekara guda.

Sun yi aure, suna farin ciki kuma suna tsammanin ɗansu na farko, lokacin da Thompson ya karɓi hotuna da ke nuna Priscilla tare da wani mutum. Hakan ya ba shi ra'ayin cewa yaudara ce ta haifar da rugujewar aure. Evelyn ta gabatar da saurayinta ga Priscilla a wani lokaci. Ta ko ta yaya ta gaskata Priscilla ta sace shi kuma shi ne a cikin hotuna tare da ita.

Tsokaci[gyara sashe | gyara masomin]

Nollywood Reinvented ya ba fim ɗin ƙimar kashi 50%.[2]

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Broken Mirror". Talk African Movies (in Turanci). 2014-11-23. Retrieved 2018-11-17.
  2. "Broken Mirror | Nollywood REinvented". Nollywood REinvented (in Turanci). 2014-10-25. Retrieved 2018-11-17.