Bruno Zita Mbanangoyé

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bruno Zita Mbanangoyé
Rayuwa
Haihuwa Port-Gentil (en) Fassara, 15 ga Yuli, 1980 (43 shekaru)
ƙasa Gabon
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Petrosport (Egypt) (en) Fassara1998-2001168
  Gabon national football team (en) Fassara1999-2012474
AS Djerba (en) Fassara2001-200510019
ES Zarzis (en) Fassara2005-2006267
FC Dinamo Minsk (en) Fassara2006-20096416
  Sivasspor (en) Fassara2009-2010173
FC Dinamo Minsk (en) Fassara2011-2012462
Missile FC (en) Fassara2013-2016
FC 105 Libreville (en) Fassara2016-2017
Sapins FC (en) Fassara2018-2018
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Nauyi 70 kg
Tsayi 172 cm

Bruno Mbanangoyé Zita (an haife shi a ranar 15 ga watan Yuli 1980) tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Gabon wanda yake taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya. Ya kasance memba na tawagar kasar Gabon.

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Zita ya fara aikinsa a ƙungiyar Petrosport kuma ya shiga cikin bazara 2001 tare da kulob ɗin AS Djerba.[1] Bayan shekaru hudu tare da AS Djerba ya sanya hannu a lokacin rani 2005 a ƙungiyar ES Zarzis. Zita ya bar Tunisiya bayan shekaru biyar kuma ya rattaba hannu da kulob din Dinamo Minsk na Belarus a watan Janairun 2006. Zita ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyu da kungiyar Sivasspor ta Turkiyya a ranar 31 ga watan Agustan 2009.

Zita ya sake sanya hannu a kulob ɗin Dinamo Minsk a cikin watan Janairu 2011. [2] Ya wakilci tawagar kasar Gabon a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 2012, inda Gabon, ta zama a matsayin mai masaukin bakin gasar, ta kai wasan daf da na kusa da karshe.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Bruno Mbanangoyé Zita - International Appearances
  2. Мбанангой и Ледесма усилили "Динамо"

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]