Callista Chimombo
Callista Chimombo | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Zomba (en) , 24 Mayu 1959 (65 shekaru) | ||
ƙasa | Malawi | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Democratic Progressive Party (en) |
Madame Callista Chapola-Chimombo (Callista Mutharika) (an haife ta 24 Mayu 1959)[1] ta kasance ‘yar siyasar Malawi ce, kuma tsohuwar matar marigayi Shugaban kasa Bingu wa Mutharika. Ta yi aiki matsayin uwar gidan shugaban kasar Malawi daga 2010 zuwa 2012. Chimombo ta kasance tsohuwar memba na Majalisar Ministocin Malawi a matsayin Mai Gudanarwa ta Kasa akan Haihuwa, Yara da Kiwon Lafiyar Yara da HIV/Abinci/Maleriya da kuma Tarin Fuka.
A halin yanzu tana aiki a matsayin Babban Kwamishinan Malawi a Jamhuriyar Kenya, ta gabatar da tsarin diflomasiyya ga shugaban Kenya a ranar 1 ga Afrilu 2022. Ta kuma yi aiki a matsayin ‘yar majalisa a Majalisar Dokokin Pan-Afirka, kuma a matsayin Ministan Yawon Bude Ido, Dabbobi da Al'adu na Malawi. [2]
Ya zuwa shekara ta 2005, ta zamo Sakatariyar Kungiyar Mata ta Malawi . [3] Chimombo tsohuwar memba ce ta Jam'iyyar Democratic Progressive kuma tsohuwar memba ce daga United Democratic Front (UDF). [4]
Rayuwarta
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Janairun 2010, bayan wani lokaci na hasashe mai tsanani, an sanar da cewa Chimombo da Shugaba Mutharika sun yi daura niyyan aure kuma za su yi aure a ranar 1 ga Mayu 2010. Sun yi alkawari a ranar masoya ta 2010 a wani bikin gargajiya wanda aka watsa a labarai. A wani lokaci, Mutharika da Callista sun nuna farin cikinsu ta hanyar kai shi filin rawa inda 'ya'yansa, danginsa da baƙi suka kwashe tsawon mintuna 20 suna rawa zuwa wani nau'i na raha da farin ciki.[1] Sun yi aure a Cocin Roman Katolika.[5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Profile of First Lady Callista Mutharika". Malawidemocrat.com. 2011-08-22. Retrieved 2012-04-16.[dead link]
- ↑ "Malawi Announces Cabinet Reshuffle". Scotland-MalawiPartnership.org. Scotland Malawi Partnership. 2007-05-11. Archived from the original on 2011-01-03. Retrieved 2007-09-09.
- ↑ "Parliamentary Centre Hosts A Southern Africa Regional Workshop On Micro Finance as Strategy for Poverty Reduction". ParlCent.ca. Parliamentary Centre of Canada. Archived from the original on 2005-07-31. Retrieved 2007-09-09.
- ↑ "List of Members of the Pan African Parliament" (PDF). Africa-Union.org. African Union. Archived from the original (PDF) on 2011-05-18. Retrieved 2007-09-09.
- ↑ Malawi's President Mutharika to marry ex-minister BBC News, 24 January 2010