Jump to content

Canjin yanayi a Nicaragua

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Hoton tauraron dan adam na yanayin fari a Nicaragua, 2015.

Sauyin yanayi yana da tasiri sosai ga kasar Nicaragua ta Tsakiyar Amurka. Sauyin yanayi zai sa Nicaragua tayi zafi da bushewa acikin karni na 21, tare da wani bincike na 2020 wanda yayi hasashen yanayin zafi acikin kasar na iya zama wanda ba za'a iya rayuwa ba ga mutane nan da 2070.

Kamar yadda yake da sauran ƙasashe a Amurka ta tsakiya, ana tunanin illar sauyin yanayi zai taimaka wajen kaura daga Nicaragua. Haka kuma yanayin zafi yana shafar noman kofi, lamarin da yasa wasu manoman ke yin gwaji da nau’o’in iri daban-daban domin amfanin gonakinsu ya samu karbuwa.

Nicaragua kungiya ce ta Kyoto Protocol kuma ta amince da yarjejeniyar Paris a cikin 2017. Tun farko kasar na daya daga cikin kasashe kalilan da ba su amince da yarjejeniyar ba, saboda adawar da wakilinta Paul Oquist ya yi na nuna rashin amincewa da gudummawar da kasashen ke yi na son rai.[1] Acikin 2022, ƙasar ta kuma amince da manufar sauyin yanayi ta kasa, wanda ke mai da hankali kan magance sauyin yanayi ta hanyar kiwon lafiya, kula da ruwa, kiyayewa da kuma amfani da albarkatu mai dorewa.

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :0