Hermenegildo António Fernandes Dinis, wanda ake yi wa lakabi da Chico Dinis (an haife shi a ranar 11, ga watan Oktoba 1958) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Angola mai ritaya. Ya taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Petro de Luanda ta Angola da kuma tawagar kasar Angola.[1]
Chico Dinis ɗan'uwa ne ga tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa Joaquim Dinis da kocin ƙwallon kwando Carlos Dinis.[2]