Jump to content

Clement Tumfuga Bugase

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Clement Tumfuga Bugase
Member of the 2nd Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 1997 - 6 ga Janairu, 2001
District: Navrongo Central Constituency (en) Fassara
Election: 1996 Ghanaian general election (en) Fassara
Rayuwa
ƙasa Ghana
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa National Democratic Congress (en) Fassara

Clement Tumfuga Bugase ɗan siyasan Ghana ne kuma memba na majalisar dokoki ta biyu na jamhuriya ta huɗu ta Ghana mai wakiltar Navrongo ta tsakiya a ƙarƙashin mambobi na National Democratic Congress (NDC).[1]

Sana'ar siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

An zabe shi a ranar bakwai 7 ga watan Janairu, shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da bakwai 1997 bayan ya zama zakara a babban zaben Ghana na shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da shida 1996. Ya doke John Setuni Achuliwor wanda ya kasance mai cin gashin kansa ta hanyar samun kashi arba'in da ɗaya da ɗigo goma 41.10 cikin ɗari 100 na jimlar kuri'u dubu sha shida da ɗari takwas da goma sha ɗaya 16,811 yayin da 'yan adawar sa suka samu kashi talatin da takwas da ɗigo goma 38.10% wanda ke daidai da kuri'u dubu goma sha biyar da ɗari biyar da casa'in da tara 15,599.[2] Bayan ya wakilci mazabarsa na tsawon shekaru hudu, Bugase ya yanke shawarar sake tsayawa takara karo na biyu inda John Setuni Achuliwor ya kayar da shi wanda ya shiga sabuwar jam'iyyar Patriotic Party kafin zaben kuma ya samu kashi arba'in da ɗaya da ɗigo hamsin 41.50% na yawan kuri'u masu inganci wanda ya yi daidai da kuri'u dubu goma sha ɗaya da ɗari biyu da arba'in da shida 11,246. yayin da Bugase ya samu kashi arba'in da ɗigo casa'in 40.90 wanda yayi daidai da kuri'u dubu goma sha ɗaya da ɗaru ɗaya da ukku 11,103. An kayar da shi ne tare da Pwoawuvi J. Weguri na babban taron jama'a, Kaguah A. Castor na National Reform Party, Frank Awepuga na Great Consolidated Popular Party, Jennifer Anemana na Convention People's Party da Margaret A. Punguse ta United Ghana Movement.[3][4][5]

  1. "Navrongo Central Constituency: Where will the pendulum swing?". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2020-10-13.
  2. FM, Peace. "Ghana Election 1996 Results - Navrongo Central Constituency". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-10-13.
  3. FM, Peace. "Ghana Election 2000 Results - Navrongo Central Constituency". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-10-13.
  4. "NPP parliamentary primaries in Navrongo Central: Aviation Minister vs Regional Minister". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2020-10-13.
  5. "Four to contest Navrongo seat". www.ghanaweb.com (in Turanci). 13 March 2003. Retrieved 2020-10-13.