Jump to content

Confucius

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Confucius
Rayuwa
Cikakken suna 孔丘
Haihuwa Qufu (en) Fassara, 551 "BCE"
ƙasa Lu (en) Fassara
Harshen uwa Historical Chinese (en) Fassara
Mutuwa Si River (en) Fassara, 479 "BCE"
Makwanci Cemetery of Confucius (en) Fassara
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi
Ƴan uwa
Mahaifi Shuliang He
Mahaifiya Yan Zhengzai
Abokiyar zama Qiguan Shi (en) Fassara
Yara
Ahali Meng Pi (en) Fassara
Karatu
Harsuna Old Chinese (en) Fassara
Sinanci
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a mai falsafa, Malami da marubuci
Wurin aiki Lu (en) Fassara
Muhimman ayyuka Analects (en) Fassara
Fafutuka Konfushiyanci
Imani
Addini Konfushiyanci
IMDb nm0174595

Confucius shi ne daya daga cikin manyan ‘yan [1] na duniya, kuma shi ya kago darikar Confucius. Dakin ibada da gida da kabari da aka gina don tunawa da Confucius su ne alamar da sarakunan kasar Sin suka kafa a shekaru dubu 2 da suka shige don nuna ban girma ga Confucius da darikar Confucius. Suna da muhimmin matsayi a cikin tarihin kasar Sin da al’adun gabashin duniya.

Dakin ibada na Confucius da gidan Confucius da kabarin Confucius suna garin Confucius wato birnin Qufu na lardin Shandong a gabashin kasar Sin.

Ana kira Dakin ibada na Confucius dakin ibada na farko a kasar Sin. A shekara ta 478 na kafin haifuwar Anabi Isa, wato shekara ta biyu bayan rasuwar Confucius, sarkin kasar Lu ya gina tsohon gidansa da ya zama dakin ibada, an ajiye tufafinsa da kayayyakinsa. A wancan lokaci, dakuna uku kawai. Daga bisani kuma al’adun darikar Confucius ya zama al’adun gaske na kasar Sin, sarakunan kasar Sin sun yi ta habaka dakin ibada na Confucius, har sun zama manyan dakuna masu kayatarwa. Ya zuwa farkon karni na 18, sarki Yongzheng na szarautar Qing ya ba da umurnin gyara dakin ibada bisa babban mataki, har ya zama irin salon da mu ke gani.

Tsawon Dakin ibada na Confucius daga kudu zuwa arewa ya kai mita dubu daya, fadinsa ya kai muraba’in kilomita dubu 100, akwai dakuna kusan 500, girmansa yana bayan tsohuwar fada ta Beijing kawai. Lallai misalin koyo ne ga dakunan ibada na kasar Sin.

An gina dakin ibada na Confucius ne bisa fasalin fadar sarki. Yana da kuma wani layin tsakiya na daga kudu zuwa arewa, an gina manyan dakuna a kan wannan layin tsakiya, kuma an gina dakuna a gefuna biyu na wannan layi. Dakin ibada na Confucius yana da hawa 9, da farfajiya 9, babban gini mai suna Dacheng yana da fadin dakuna 9. Da ma sai sarki yana da ikon yin amfani da 9 don gina fadar sarki, idan farar hula su gina gida mai dakuna 9, to ya taka doka ke nan, za a yanke masa hukuncin kisa, amma dakin ibada na Confucius halal ne. An gina babbar kofar dakin ibada na Confucius ne bisa tsarin fadar sarki, wato hawa 5.

Babban daki mai suna Dacheng shi ne cibiyar dakin ibada na Confucius, tsawonsa ya kai mita 30, fadinsa daga gabas zuwa yamma ya kai fiye da mita 50, kuma an gina rawayen rufi, yana da kayatarwa irin na fadar sarki. A gaban babban dakin nan kuma akwai manyan ginshikan duwatsu 10 da aka yi sassakar dodo, irin kyaunsa ya kai fiye da na tsohuwar fada.

A cikin dakin ibada na Confucius kuma an ajiye manyan duwatsu fiye da dubu 2 da aka sassaka bayani. Duwatsun da aka sassaka bayanonin da sarakuna suka rubuta sun kai fiye da 50, wannan sosai ya shaida matsayi mai daukaka na Confucius a kan tarihin kasar Sin.

Gidan Confucius yana dab da dakin ibada na Confucius, wato gida ne na jikokin Confucius. Shi ne babban gidan da ke bayan fadar sarki kawai.

An fara gina gidan Confucius ne a sarautar Song wato a karni na 12, fadinsa ya kai muraba’in mita dubu 50, gidan nan yana da dakuna kusan 500. Gidan Confucius yana da salon musamman, a gaban gidansa dakuna ne na yin harkokin gwamnati, a baya kuma dakuna ne na zaman yau da kullum. Irin dakunan karbar baki suna da surar sarautar Ming da Qing. A cikin gidan Confucius akwai takardun tarihi da tufafi da kayayyaki na zamanin da masu daraja da yawa.

Kabarin Confucius kabarin musamman ne da aka binne jikokin Confucius, shi ne kabarin da ya fi girma da ya fi dade a duniya. An yi amfani da wurin nan don binne jikokin Confucius har cikin shekaru dubu 2 da 500, fadinsa ya kai muraba’in kilomita 2, akwai karburbura fiye da dubu 100 na jikokin Confucius, kuma an kafa duwatsu fiye da dubu 5 da aka sassaka bayanoni.

Kabarin Confucius yana da amfani kwarai a wajen bincike ci gaban siyasa da tattalin arziki da al’adu da jana’iza na zamani daban daban na kasar Sin.

Dakin ibada da gida da kabari na Confucius sun shahara a duk duniya ba sabo da kayayyakin al’adu masu dimbin yawa kawai ba, kuma sabo da halitattun abubuwa. Misali a wurin nan akwai tsofaffin itatuta fiye da dubu 17 wadanda ke shaida dadadden tarihi na darikar Confucius, kuma suna da amfani kwarai a wajen bincike yanayi da halita na tsohon zamani.

Dakin ibada da gida da kabari na Confucius suna da kayayyakin al’adu da yawa, kuma da dadadden tarihi, sabo da haka suna da babbar daraja a wajen bincike kimiya da fasaha. A shekara ta 1994, kwamitin kayayyakin gado na duniya na kungiyara UNESCU ya nada dakin ibada da gida da kabari na Confucius da ya zama kayayyakin gado na duniya.

  1. https://iep.utm.edu/confucius/