Jump to content

Congress of Nigerian University Academics

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Congress of Nigerian University Academics
Bayanai
Iri ma'aikata

Congress of Nigerian University Academics (CONUA) wata kungiyace da ta ɓalle daga Ƙungiyoyin Ma'aikatun Jami'o'i (ASUU) ta Najeriya.[1][2][3][4] Kungiyar na ƙarƙashin jagorancin Niyi Sunmonu daga Jami'ar Obafemi Awolowo. An kafa ta ne a shekara ta 2018 kuma sai a watan Oktoban 2022 Ministan Kwadago da Aiki Sanata Chris Ngige ya amince da ita ne sakamakon gazawar gwamnatin tarayyar Najeriya da Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya na kasa cimma matsaya da za ta iya kawo karshen yajin aiki na tsawon makonni talatin da uku wanda aka fara tun a cikin watan Fabrairun 2022.[5][6][7][8]

Wadanda suka kafa CONUA sun fito ne daga jami'o'i biyar wadanda su ne;[1]

  • Obafemi Awolowo University (OAU),
  • Ambrose Alli University (AAU),
  • Ekpoma Jami'ar Tarayya, Oye Ekiti (FUOYE);
  • Jami'ar Tarayya, Lokoja (FUL) da Kwara State University (KWASU), Molete