Connecticut v. ExxonMobil Corp.

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Connecticut v. ExxonMobil Corp shari'a ce ta canjin yanayi da'aka kawo kan ExxonMobil don neman riba dukda sanin ɓarnar dazai haifar akan muhalli.

A ranar Litinin, 15 ga Satumba, 2020, Babban Lauyan Connecticut William Tong ya shigar da ƙara ƙarfi a kan ExxonMobil saboda kayayyakinsu sun bada gudummawar hayaki dake haifar da ɗumamar yanayi da sauyin yanayi.Jihar na neman diyya ga abubuwan da suka faru a baya, na yanzu da kuma nan gaba daga canjin yanayi, ciki harda zuba jari da aka riga akayi, kuma tana bin wasu ribar da kamfanin ya samu.

Connecticut ta zargi ExxonMobil game da yaudarar masu saka hannun jari kan yadda samfuransu ke bada gudummawa ga canjin yanayi. Tong yace jihar na fuskantar miliyoyin daloli a cikin lalacewa saboda hauhawar matakan teku, da karin guguwa, da kara zazzagewa da sauran tasirin sauyin yanayi.Tong yayi iƙirarin ExxonMobil ya san cewa kona burbushin halittu yana shafar muhalli, amma maimakon yarda da shi, suna ƙoƙarin yaudarar jama'a. An shigar da karar zuwa Kotun Ƙoli ta Hartford.

A halin yanzu, shari'ar da ke akwai tsakanin jihar Connecticut da ExxonMobil Corp. har yanzu ba a daidaita ba, har yanzu ba a sami wani diyya ga jihar ba. Bayan shigar da karar a shekarar 2020, alkalin kotun Richard Sullivan ya bayyana a shekarar 2022, cewa idan aka yi la’akari da wahalar ire-iren wadannan shari’o’in, kotun jihar na iya jayayya cewa Connecticut ba ta da hurumin ci gaba da asarar da dumamar yanayi ta haifar daga. a cikin rabin karni/ƙarni na ƙarshe.