Jump to content

Dahiru Bako Gassol

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Dahiru Bako Gassol
mutum
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Shekarun haihuwa 4 Mayu 1954
Wurin haihuwa Gassol
Sana'a ɗan siyasa
Muƙamin da ya riƙe mamba a majalisar dattijai ta Najeriya
Ɗan bangaren siyasa Peoples Democratic Party

Dahiru Bako Gassol' (an haife shi a ranar 4 ga watan Mayu,shekara ta alif ɗari tara da hamsin da hudu 1954A.c) an zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Taraba ta tsakiya a jihar Taraba dake Najeriya, ya karɓi mulki a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007. Ɗan jam'iyyar PDP ne.[1]

Gassol ya kuma samu Difloma a fannin Gudanarwa. An kuma naɗa shi Darakta, kula da lafiya a matakin farko na ƙaramar hukumar Bali a jihar Taraba. An zaɓe shi a Majalisar Wakilai a shekara ta 1999, kuma ya sake zaɓe a 2007.[1] Bayan ya hau kujerar majalisar dattawa, an naɗa shi kwamitocin kula da albarkatun ruwa, ayyukan majalisar dattawa, al’adu da yawon buɗe ido da kasuwannin jari.[1] A wani nazari na tsakiyar wa’adi na Sanatoci a cikin watan Mayun shekarar 2009, Thisday ya ce bai ɗauki nauyin wani ƙudiri ba, kuma da kyar ba a iya gani a ƙasa ko a cikin kwamitin.[2]

An naɗa Gassol shugaban ƙungiyar ƴan majalisar dokokin jihar Taraba. A wata hira da aka yi da shi a cikin watan Janairun shekarar 2010, ya bayyana cewa ƴan majalisar na da kyakkyawar alaƙa da Gwamna Danbaba Suntai.[3]