David Raum

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
David Raum
Rayuwa
Haihuwa Nuremberg, 22 ga Afirilu, 1998 (26 shekaru)
ƙasa Jamus
Karatu
Harsuna Jamusanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Germany national under-19 football team (en) Fassara13 Nuwamba, 2016-9 ga Yuli, 201751
  SpVgg Greuther Fürth (en) Fassara1 ga Faburairu, 2017-
  Germany national under-20 football team (en) Fassara4 Satumba 2017-27 ga Maris, 201860
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Tsayi 180 cm

David Raum an haife shi a ranar 22 ga watan Afrilu a shekarar 1998 ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Jamus wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya na hagu ko kuma na hagu don ƙungiyar RB Leipzig da ke Bundesliga da kuma ƙungiyar kwallon kafar ƙasar Jamus.[1]

Aikin Kulob[gyara sashe | gyara masomin]

Greuther Fürth[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Raum a garin Nuremberg kuma ya fara wasan kwallon kafa a kulob en gida mai suna Tuspo Nürnberg sadda ya kai shekaru 4 da haihuwa.[2] Sadda Raum ya kai shekara 4, an zabe shi zuwa shiga kungiyar matasa na SpVgg Greuther Fürth wanda ke cikin makwabtan gari sannan ya samu cigaba da daukaka zuwa kungiyoyin matasa da dama.

A matsayin dan wasan kasa da shekara 19, watau U-19 kenan, Raum ya samu gogewa da farkon samun shigar sa cikin manyan wasan kuma yana cikin kungiyan farkon team na shekarar 2017–18 a Bundesligar Jamus. Ya kuma zura kwallaye a cikin farkon fafatawa 2 da aka yi na gasar DFB-Pokal na shekarar 2017–18, amma bai samu kai ga zuwa wasan karshe ba dalilin gaza cin FC Ingolstadt da su kayi.[3] Baya ga haka kuma, Raum ya buga wasa 20 a cikin kungiyar na Jamus amma a matsayin dan chanji yake futowa a shekarun da suka bi baya. Kuma an bashi daman kara Kwantaragin sa wanda zai kare a ranar 5 ga watan Yunin a shekarar 2020.[4]

TSG Hoffenheim[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan kakar 2020–21, wanda kungiyar Greuther Fürth suka samu daukaka zuwa Bundesliga, Raum ya koma TSG Hoffenheim a free transfer, bayan ya saka hannu a kwantaragi a kungiyar a watan Janirun 2021. Sannan ya saka hannu a kwantaragin shekaru 4 da kungiyar Die Kraichgauer.[5]

RB Leipzig[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 31 ga watan Yulin 2022, ya saka hannu ga kungiyar RB Leipzig wanda ke a Bundesliga ta Jamus akan kwantaragin shekara 5 har zuwa 2027.[6]

Aikin Kasa[gyara sashe | gyara masomin]

Raum ya buga wasa 11 a kungiyar kasar under-19 da kuma under-20.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]