Davy Van Den Berg

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Davy Van Den Berg
Rayuwa
Cikakken suna Dave Johannes Andreas van den Berg
Haihuwa Uden (en) Fassara, 4 ga Faburairu, 2000 (24 shekaru)
ƙasa Kingdom of the Netherlands (en) Fassara
Harshen uwa Dutch (en) Fassara
Karatu
Harsuna Dutch (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Jong FC Utrecht (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya

Davy Van Den Berg[1] Dave Johannes Andreas van den Berg an haife shi a ranar 4 ga watan Fabrairu a shekarar 2000 ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Netherlands wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar PEC Zwolle na league din Eredivisie.[2]


Shekarun farko[gyara sashe | gyara masomin]

Van den Berg ya buga wasan kwallon kafa na matasa a kungiyar UDI '19, kafin ya shiga makarantar koyon kwallon matasa ta PSV Eindhoven a 2008.[3]

A ranar 3 ga watan Oktoban 2018, Van den Berg ya kasance cikin kungiyar PSV ta U-19 da ke fafatawa a UEFA Youth League, karkashin babban koci Ruud van Nistelrooy. Ya fara buga wasansa na farko a gasar da Inter Milan ta ‘yan kasa da shekara 19, inda ya zo a matsayin dan chanji a madadin Rico Zeegers a ci 2-1. A ƙarshen 2018, Van den Berg ya samu sabani da kocinsa Van Nistelrooy ba, kuma an dakatar da kwangilarsa ta hanyar amincewar juna.[4]


Ya shiga addinin Musulunci kuma yana burge mutane a kafafen sada zumunta tare da karatun Alqur'ani mai Girma, musamman inda matashin dan shekara 22 yana karanta ayoyi daga Suratul Nazi’at.[5]


Utrecht[gyara sashe | gyara masomin]

Van den Berg ya koma FC Utrecht a ranar 13 ga watan Fabrairun 2019 akan canja wuri kyauta, watau free transfer kenan inda ya rattaba hannu kan kwantiragi har zuwa 2021 tare da zaɓi na ƙarin shekara.[6] Ya fara buga wasansa na farko ga kungiyar rejin Jong FC Utrecht, inda ya fafata a matakin na biyu na Eerste Divisie, a ranar 18 ga watan Oktoban 2019 a wasan da suka tashi 2-2 gida da De Graafschap, wanda ya shigo a madadin dan chanji ga dan wasannan Hicham Acheffay.


A ranar 9 ga Satumba 2020, an tsawaita kwantiraginsa har zuwa 2023 gami da zaɓi na ƙarin shekara.[7]

Ya buga wasansa na farko na Eredivisie a Utrecht a ranar 29 ga watan Agustan 2021 a matsayin dan chanji a wasan da suka yi da kungiyar Feyenoord.

A ranar 31 ga watan Janairun 2022, an ba da aron van den Berg zuwa kungiyar Roda JC Kerkrade.

PEC Zwolle[gyara sashe | gyara masomin]

Van den Berg ya shiga kungiyar PEC Zwolle a ranar 4 ga watan Agustan 2022, inda ya rattaba hannu kan kwangilar shekaru biyu tare da zaɓi na ƙarin shekara. Ya buga wasansa na farko a kulob din a ranar 7 ga watan Agusta, inda ya fito daga benci don maye gurbin Tomislav Mrkonjić a rabin lokacin gasar lig da ta doke De Graafschap da ci 2-1.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://en.m.wikipedia.org/wiki/Davy_van_den_Berg
  2. https://www.vi.nl/spelers/davy-van-den-berg/profiel
  3. https://www.ed.nl/psv/fc-utrecht-neemt-davy-van-den-berg-19-definitief-over-van-psv~ac910b17/
  4. https://www.rodajckerkrade.nl/nieuwsbericht/31-03-2022/davy-gunt-de-roda-jc-fans-promotie-van-harte
  5. https://islamchannel.tv/blog-posts/video-watch-dutch-muslim-convert-footballer-davy-van-den-berg-recites-the-quran
  6. https://utrecht.nieuws.nl/sport/70727/davy-van-den-berg-sluit-aan-bij-jong-fc-utrecht/
  7. https://www.fcupdate.nl/voetbalnieuws/339432/psv-onder-19-wordt-beloond-en-wint-laat-van-inter/