Dazuzzuka na Karni na 21st

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Dazuzzuka na Karni na 21st
Asali
Lokacin bugawa 2009
Ƙasar asali Birtaniya
Distribution format (en) Fassara direct-to-video (en) Fassara
Characteristics
Genre (en) Fassara documentary film

Dazuzzuka na karni na 21 ɗan gajeren bidiyo ne dake haɓɓakawa da kuma bayyana fa'idodin gyaran gandun daji. Acikin 'yan ƙarnuka da suka wuce, mutane sun kawar da fiye da rabin dazuzzukan duniya.[1]Yanke dazuzzuka a halin yanzu, shine ke da alhakin kusan kashi 20 cikin 100 na hayakin carbon a duniya.Za'a iya jujjuya wannan guguwar saren gandun dajin, amma zamu iyayin tasiri sosai idan muka sake mayar da wasu dazuzzukan da muka rasa. Dasa bishiyoyi da yawa na iya kulle ƙarin carbon, inganta yanayi da rayuwar mutane. Yawancin yankuna da ƙasashe sun riga sun maido da dazuzzuka da yawa.

Taƙaitawa[gyara sashe | gyara masomin]

Fim ɗin ya ƙunshi misalan ayyukan gyara da aka yi nasara a Burtaniya, a Shinyanga da ke arewacin Tanzaniya da kuma yankin Miyun na China. Sabbin bayanai sun nuna cewa akwai miliyoyin kadada da yawa na dazuzzukan da suka lalace da kuma gurɓatattun filayen da suka dace da maidowa fiye da kiyasin da aka yi a baya.[2] An kwatanta girman damar duniya don dawo da gandun daji a cikin bidiyon a karon farko.

Hukumar kula da gandun daji ta Biritaniya da IUCN ne suka shirya fim ɗin na mintuna 15 a watan Nuwamba 2009 a madadin Ƙungiyar Haɗin Kan Duniya kan Maido da yanayin gandun daji.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "IPCC 4th Assessment Report". Archived from the original on 2018-11-02. Retrieved 2023-09-16.
  2. "GPFLR - A World of Opportunity" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2011-07-26. Retrieved 2023-09-16.

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]