Du Shuzhen

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Du Shuzhen
Rayuwa
Haihuwa Kaifeng (en) Fassara, 1924 (99/100 shekaru)
ƙasa Sin
Sana'a
Sana'a Liman
Amina

Du Shuzhen ( Chinese  ; An haife ta ne a shekara ta 1924), kuma anfi saninta da Amina, limamin kasar Sin shine kawunta. Da taimakon kawunta da wata kawarta, wadanda dukkansu limamai ne a Shanghai da Henan, bi da bi, ta koyi karatun al'kur'ani a cikin harshen Larabci . Sannan ta yi aikin Hajjin farko a shekara ta 1992, inda ta zama mace ta farko a Henan.

Rayuwarta ta farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Du a cikin shekara ta 1924 a Kaifeng, Henan, China. An rada mata sunan islamiyyan Aminah (埃米乃). Mahaifinta, musulmi dan kabilar Hui, ya zama limami bayan da aka sace masa kantin kayan tarihi a lokacin yakin Sino da Japan na biyu, yayin da mahaifiyarta ta rasu kafin Du ta mallaki hankalinta matashiya. [1] Bayan mutuwar mahaifiyarta, Du ta koma wurin innanta. [2] Tana da shekaru takwas, Du ta shiga masallacin mata na yankin, inda ta yi karatun addinin Islama na wasu shekaru shida. [1] A bisa ga burin mahaifinta, tana da shekaru goma sha biyar, Du ta auri wani malami musulunci dan kasar Sin. Bata son auren amma duk da haka ta bi mijinta zuwa Shanxisannan mijinta ya mutu ne bayan shekaru biyu; ta ki kara aure, Du ta koma Kaifeng, inda ta ci gaba da karatunta acikin masallacin da fatan ta zama limamiya da kanta. [1] Yan uwanta ba su yarda da shawarar da ta yanke ba.

Sana'arta[gyara sashe | gyara masomin]

A baya a Kaifeng, Du ta kammala karatunta na islamiyya a harshen Farisa karkashin kulawar wata limamiya mace. Tare da taimakon kawunta da wata kawarta, wadanda dukkansu limamai ne a Shanghai da Henan bi da bi, ta kuma koyi karatun kur'ani a cikin harshen Larabci . [1] A cikin shekara ta 1949, Du ta zama limamiya a Masallacin Shifu da ke Zhengzhou . [3] Daga baya Du ta yi aiki a wasu masallatan mata a fadin kasar Sin, ciki har da Kaifeng, Xingyang, da Xi'an . [3] A lokacin juyin juya halin al'adu, Du ta nemi mafaka a masallacin gabas a garinsu. [1] A cikin shekara ta 1981, an nada ta a matsayin babbar malamar addinin musulunci a masallacin mata na titin Beida a Zhengzhou. Bayan shekara biyu aka kara mata girma zuwa limamiyar masallacin. [1] Du ta gudanar da aikin Hajjinta na farko a shekara ta 1992, [1] ta zama mace ta farko a Henan. [2] Ta sake yin aikin hajji sau uku, a skekara ta 1994, 1999, da 2005. Du ta kasance mai himma sosai a matsayinta na jagoran addinin Musulunci a kasar Sin, kuma ta kasance memba na kungiyoyi da dama, ciki har da kungiyar Islama ta lardin Henan, da kungiyar Islama ta birnin Zhengzhou, da kungiyar musulinci ta kasar Sin. [3]

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

 

ambato[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 1.6 Lee 1998.
  2. 2.0 2.1 Jaschok & Shui 2013.
  3. 3.0 3.1 3.2 Jaschok & Shui 2012.