Edith Hazel
Edith Hazel | |||
---|---|---|---|
7 ga Janairu, 2001 - 6 ga Janairu, 2005 District: Evalue-Gwira (en) Election: 2000 Ghanaian general election (en) | |||
Rayuwa | |||
ƙasa | Ghana | ||
Karatu | |||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | National Democratic Congress (en) |
Edith Hazel ƴar siyasar ƙasar Ghana ce kuma jami'ar diflomasiyya, wacce ta yi aiki a matsayin yar majalisar dokoki ta mazaɓar Evalue Gwira a Yankin Yammacin Ghana daga shekara ta (2001 zuwa shekara ta 2005) .[1][2]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Hazel ta halarci Jami'ar Ghana.[2] Har zuwa lokacin da aka nada ta a matsayin jakadiyar Ghana a Denmark da Finland[3] a watan Yulin shekara ta (2014) , ta rike mukamin mataimakiyar shugaban tawagar Ghana a Washington, D.C., U.S.[2]
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]An zabi Hazel a matsayin mamba na majalisar mazabar Evalue Gwira da ke Yankin Yammacin Ghana a babban zaben Ghana na shekara ta (2000),Don haka ta kasance a matsayin memba na majalisa ta( 3 ),na jamhuriyya ta (4 ),da kuri'u (6,598), tare da kwatankwacin kashi (42.80%), akan tikitin National Democratic Congress.
Ta rasa kujerar ta a shekara ta (2004), a hannun Kojo Armah.[4][5][6] An zabe ta akan Kojo Armah na Jam'iyyar Convention Peoples Party, Sagary Nokoe na New Patriotic Party, Nana Kwabena Erskine na Jam'iyyar Reform Party.[7] Wadannan sun samu kuri'u( 5,994, 2,702), da kuri'u( 115), daidai da jimillar kuri'un da aka kada.[7] Waɗannan sun yi daidai da( 38.90%, 17.50% da 0.70%) bi da bi na jimillar ƙuri'un da aka jefa.[7]
An zabi Hazel akan tikitin National Democratic Congress.[2] Jam'iyyar National Democratic Congress ta lashe jimillar kujerun majalisa( 9), daga cikin kujeru (19), na Yankin Yammacin kasar a wannan zabubbukan.[8] A cikin duka, jam'iyyar ta sami rinjaye na wakilai (89), daga cikin kujeru( 200), a majalisar( 3), ta jamhuriya ta (4) ta Ghana.[8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Ghana MPs - List of 2013 - 2017 (6th Parliament) MPs". www.ghanamps.com. Retrieved 2020-09-02.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 2.3 "Former Ghana Ambassador Meets LDS Leaders". news-gh.churchofjesuschrist.org (in Turanci). 2018-02-15. Retrieved 2020-09-04.
- ↑ Minister calls for closer ties with Finland
- ↑ "Edith Hazel | C-SPAN.org". www.c-span.org. Retrieved 2020-09-02.
- ↑ FM, Peace. "Parliament - Western Region Election 2000 Results". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-09-02.
- ↑ GHDiaspora (2017-02-03). "NDC Finland bids farewell to Ghana Ambassador to Denmark". GH Diaspora (in Turanci). Archived from the original on 2020-09-26. Retrieved 2020-09-02.
- ↑ 7.0 7.1 7.2 FM, Peace. "Ghana Election 2000 Results - Evalue Ajomoro Gwira Constituency". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-09-03.
- ↑ 8.0 8.1 FM, Peace. "Ghana Election 2000". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-09-02.