Elizabeth Ofili
Elizabeth Ofili | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Najeriya, 1956 (67/68 shekaru) |
Karatu | |
Makaranta |
Johns Hopkins University (en) Jami'ar Ahmadu Bello |
Sana'a | |
Sana'a | likita da cardiologist (en) |
Employers | Washington University in St. Louis (en) |
Elizabeth Odilile Ofili (an haife ta a ranar 3 ga watan Agustan 1956) likita ce yar Najeriya-Ba’amurukiya. kwararra ce a fannin sanin matsalolin zuciya. Ita ce mace ta farko da ta fara zama shugaba kungiyar likitocin cututtukan zuciya. Ita ce mace ta farko data zama shugaba a kungiyar likitocin zuciya bakaken fata a Amurka.[1][2]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Ofili a Najeriya kuma anan ta girma, ta halarci Jami'ar Ahmadu Bello don karatun likitanci. Ta koma kasar Amurka a 1982 kuma ta sami digirinta na biyu a fannin lafiyar jama'a daga Jami'ar Johns Hopkins a 1983. Ta kammala karatun digirinta na biyu a Tulsa, Oklahoma.
nasarori da kuma bincike
[gyara sashe | gyara masomin]Ofili ta fara samun ci gaba da wani bincike data gabatar a Jami'ar Oral Roberts a birnin Tulsa, a lokaci guda tana ayyukan binciken matsalolin fannin zuciya, har yau kuma farfesa a jami'ar Washington. A shekarar 1994 ta zama makaddashin farfesa a Morehouse School of Medicine.