Emmanuel Adjei Anhwere
|
| |||||
7 ga Janairu, 2021 - District: Atwima Nwabiagya South Constituency (en) Election: 2020 Ghanaian general election (en)
7 ga Janairu, 2017 - 6 ga Janairu, 2021 District: Atwima Nwabiagya South Constituency (en) Election: 2016 Ghanaian general election (en) | |||||
| Rayuwa | |||||
| Haihuwa | Mampong, 20 Satumba 1962 (63 shekaru) | ||||
| ƙasa | Ghana | ||||
| Karatu | |||||
| Makaranta |
Kwame Nkrumah University of Science and Technology Master of Business Administration (en) Jami'ar Ilimi, Winneba Bachelor in Business Administration (en) | ||||
| Harsuna | Turanci | ||||
| Sana'a | |||||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||||
| Imani | |||||
| Addini | Kiristanci | ||||
| Jam'iyar siyasa | New Patriotic Party | ||||

Emmanuel Adjei Anhwere, (an haifeshi a ranar ishirin 20 ga watan satumba, shekarata alif dubu daya da dari tara da sittin in da biyu 1962) ɗan siyasan Ghana ne kuma ɗan majalisa a majalisar dokoki ta bakwai na jamhuriya ta huɗu ta Ghana da majalissar Ghana ta 8, mai wakiltar al'ummar mazabar Atwima-Nwabiagya ta Kudu Ashanti yankin Ghana.[1]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Anhwere ya sami BBA daga Jami'ar Education Winneba, a shekarar dubu biyu da goma 2010. Ya wuce Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah inda ya sami CEMBA (Public Administration) a 2015.[2]
Aiki da Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin 2016, Anhwere ya tsaya a kan tikitin New Patriotic don zabar dan majalisa a majalisa ta 7 na jamhuriya ta hudu. Ya lashe zaben ne da kuri'u dubu arba’in da takwas da dari biyu da sittin da hudu 48,264 cikin kuri'u dubu hamsin da takwas da dari uku da goma sha’uku 58,313 da aka kada, wanda ke wakiltar 83.15% yayin da babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar National Democratic Party (NDC) Nana Asare Bediako, ya samu kuri'u 9,780, wanda ya wakilci kashi 16,85%. Ya ci gaba da rike kujerarsa a shekarar dubu biyu da ishirin 2020. Babban zaben da zai wakilci mazabarsa a majalisa ta 8 a jamhuriya ta hudu. Har zuwa zabensa a shekarar dubu biyu da goma sha’shidda 2016, ya kasance babban jami'in kula da ingancin kayayyaki na CCOBOB reshen Kumasi.[3]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Emmanuel magidanci ne mai ‘ya’ya biyar. Shi Kirista ne kuma yana bauta tare da cocin Anglican.[4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Atwima Nwabiagya, South[Ashanti-Region]. "Atwima Nwabiagya South[Ashanti-Region]". .graphic.com.gh. Graphic Communications Group. Retrieved 6 June 2017.
- ↑ "Ghana MPs - MP Details - Agyie Anhwere, Emmanuel". www.ghanamps.com. Retrieved 2021-01-10.
- ↑ "Ghana MPs - MP Details - Agyie Anhwere, Emmanuel". www.ghanamps.com. Retrieved 2021-01-10.
- ↑ "Ghana MPs - MP Details - Agyie Anhwere, Emmanuel". www.ghanamps.com. Retrieved 2021-01-10.