FC Bayern Munich
| Bayanai | |
|---|---|
| Iri | sports club (en) |
| Masana'anta | sporting activities (en) |
| Ƙasa | Jamus |
| Aiki | |
| Member count (en) | 432,500 (2 Nuwamba, 2025) |
| Mulki | |
| Shugaba | Jan-Christian Dreesen (en) |
| Babban mai gudanarwa | Herbert Hainer (en) |
| Hedkwata | München da Säbener Straße (en) |
| Subdivisions | |
| Tsari a hukumance | eingetragener Verein (mul) |
| Sponsor (en) | Deutsche Telekom (en) |
| Mamallaki na | FC Bayern München AG (en) |
| Tarihi | |
| Ƙirƙira | 27 ga Faburairu, 1900 |
| Awards received | Team of the Year (1967) Team of the Year (2001) Team of the Year (2013) Team of the Year (2020) |
| fcbayern.com
| |










FC Bayern Munich wata babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ce daga birnin Munich a ƙasar Jamus. An kafa ta a shekarar 1900 kuma tana daga cikin ƙungiyoyin da suka fi samun nasara a duniya.[1]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]An kafa Bayern Munich ne a ranar 27 ga Fabrairu, 1900, ta wasu matasa 'yan wasa 11 ƙarƙashin jagorancin Franz John. A farkon shekarun ta, ƙungiyar ba ta da karfi sosai, amma daga baya ta fara samun nasarori musamman bayan Yaƙin Duniya na Biyu.[2]
A shekarar 1965 ne Bayern ta fara taka leda a gasar Bundesliga, kuma daga nan ne ta fara zama ƙungiya mai ƙarfi a Jamus.[3]
Nasarori
[gyara sashe | gyara masomin]Bayern Munich ita ce ƙungiya mafi nasara a gasar Bundesliga, inda ta lashe gasar fiye da sau 30. Haka kuma ta lashe gasar zakarun Turai (UEFA Champions League) sau da dama.[4]
Wasu daga cikin manyan nasarorin su sun haɗa da:
- Bundesliga
- DFB-Pokal
- UEFA Champions League
- FIFA Club World Cup[5]
Filin wasa
[gyara sashe | gyara masomin]Bayern Munich na buga wasanninta a filin wasan Allianz Arena, wanda aka buɗe a shekarar 2005. Filin yana ɗaukar dubban magoya baya kuma yana daga cikin mafi kyau a Turai.[6]
Fitattun 'yan wasa
[gyara sashe | gyara masomin]A tarihin Bayern Munich, akwai fitattun 'yan wasa da dama kamar:
- Franz Beckenbauer
- Gerd Müller
- Oliver Kahn
- Thomas Müller
- Robert Lewandowski[7]
Koci-koci
[gyara sashe | gyara masomin]Wasu daga cikin shahararrun kocin da suka jagoranci Bayern Munich sun haɗa da:
- Udo Lattek
- Ottmar Hitzfeld
- Pep Guardiola
- Hansi Flick[8]
Tasiri
[gyara sashe | gyara masomin]Bayern Munich tana da tasiri sosai a duniya ta fuskar kasuwanci da kuma ci gaban wasan ƙwallon ƙafa. Tana ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka fi samun kuɗi a duniya.[9]