Falone Sumaili
Falone Sumaili | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Burundi, 1 ga Janairu, 2001 (23 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
ƙasa | Burundi | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka |
Falone Sumaili (an haife ta a ranar 16 ga watan Yuni 2001) 'yar wasan ƙwallon ƙafa ce 'yar ƙasar Burundi wacce ke taka leda a matsayin 'yar wasan gaba a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Huddersfield Town da kuma ƙungiyar mata ta Burundi.
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Sumaili a Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo a shekara ta 2001, duk da haka, an tilasta wa danginta ƙaura zuwa Burundi saboda yakin Kongo na biyu, kafin daga bisani ta nemi izinin zama 'yar gudun hijira a Burtaniya. [1] Ta fara shiga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata tana da shekaru sha shida bayan shekaru tana buga ƙwallon titi tare da yaran. Kawun nata da kakanta duk sun buga kwallon kafa, amma mahaifiyarta tana da shakku. [2]
Aikin kulob
[gyara sashe | gyara masomin]Sumaili ta fara aikinta a Burundi tare da kulob ɗin La Columbe. [3] Ta buga wasan ƙwallon ƙafa a ƙasashen Uganda da Tanzania. [1] Ta koma Ingila a matsayin 'yar gudun hijira kuma ta rattaba hannu kan Bradford City a cikin shekarar 2018. Ta ci hat-trice a ranar buɗe gasar a kakar 2019-20, kuma ta ci kwallaye 13 a wasanni 33 da ta buga, wanda hakan ya sa ta zama 'yar wasa mafi zura kwallo a kulob ɗin. [1] [4] [5]
Sumaili ta koma Huddersfield Town a lokacin rani 2021. [6] A cikin shekarar 2022, ta zira kwallaye 16 a wasanni 17 don Ƙungiyar Ci gaban su. [7] Tare da Ƙungiyar Ci gaba, ta kai wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin Sheffield da Hallamshire County. Ta samu kiran zuwa tawagar farko a gasar cin kofin 2022. [8] Ta buga wasanni 6 a kungiyar farko a kakar 2022-23. [7]
Ayyukan ƙasa da ƙasa
[gyara sashe | gyara masomin]Sumaili tana taka leda a kungiyar mata ta kasar Burundi. Ta halarci gasar cin kofin mata ta CECAFA ta shekarar 2022 a matsayi na biyu. Ta kuma taka leda a gasar cin kofin Afrika ta mata ta shekarar 2022 a matakin rukuni, karon farko da Burundi ta buga gasar. [5] [9]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 Howorth, Alasdair (10 July 2022). "Falone Sumaili: From Bujumbura to Rabat, via Bradford". Her Football Hub. Archived from the original on 22 August 2023. Retrieved 23 July 2022.
- ↑ "Burundi to Bradford: Lighting up the Women's Football League". copa90.com. Archived from the original on 2021-10-19. Retrieved 2024-03-24.
- ↑ Mehrish, Akshat (7 December 2022). "Falone Sumaili: From fleeing war-torn DR Congo to WAFCON with Burundi". FIFA. Archived from the original on 1 February 2023. Retrieved 22 August 2023.
- ↑ "Sumaili hat-trick gets Bradford City Women off to a flier". Bradford Telegraph and Argus.
- ↑ 5.0 5.1 Musembi, Peter (27 June 2022). "Women's Afcon 2022: Burundi striker Falone Sumaili unfazed by Africa's heavyweights". BBC Sport. Archived from the original on 13 July 2022. Retrieved 22 August 2023.
- ↑ Gott, Khya (31 August 2021). "CATCH UP: Town Devs Pre-Season". Archived from the original on 6 November 2021. Retrieved 24 March 2024.
- ↑ 7.0 7.1 "Falone Sumaili Player Stats". The FA. Archived from the original on 22 August 2023. Retrieved 22 August 2023.
- ↑ "TOWN WOMEN IN CUP FINAL ACTION ON SATURDAY". HTAFC. 28 April 2022. Archived from the original on 22 August 2023. Retrieved 22 August 2023.
- ↑ Mehrish, Akshat (22 October 2022). "Flight of the Swallows: Burundi Women's team bringing joy to a nation". FIFA. Archived from the original on 5 February 2023. Retrieved 22 August 2023.