Fezbuk

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Facebook
Screen of Facebook.PNG
social networking service, data collection system
farawa4 ga Faburairu, 2004 Gyara
nameFacebook Gyara
named afterface book Gyara
founded byAndrew McCollum, Mark Zuckerberg, Eduardo Saverin, Dustin Moskovitz, Chris Hughes Gyara
ƙasaTarayyar Amurka Gyara
wuriMenlo Park Gyara
owned byFacebook, Inc. Gyara
subsidiaryFacebook Developer Circles Gyara
wurin hedkwatarMenlo Park Gyara
maƙirƙiriMark Zuckerberg Gyara
mawallafiMark Zuckerberg, Eduardo Saverin, Dustin Moskovitz, Chris Hughes Gyara
harshen aiki ko sunamultiple languages Gyara
award received'Verschlossene Auster' award Gyara
operatorFacebook, Inc. Gyara
side effectrumor, vaccine controversies Gyara
product or material producedFacebook Pixel, Facebook Custom Audience, Facebook Ads Gyara
programming languagePHP Gyara
official appFacebook Android App Gyara
official websitehttps://www.facebook.com, https://www.facebookcorewwwi.onion/ Gyara
official bloghttps://about.fb.com/news/ Gyara
terms of service URLhttps://www.facebook.com/terms.php Gyara
privacy policy URLhttps://www.facebook.com/about/privacy Gyara
hashtagFacebookDown Gyara
tarihin maudu'ihistory of Facebook Gyara
Stack Exchange taghttps://stackoverflow.com/tags/facebook Gyara
Wikidata propertyFacebook ID, Facebook Places ID, Facebook ID name/number Gyara
search formatter URLhttps://www.facebook.com/search/top/?q=$1 Gyara
fazbuk

An dai kafa shafin sadarwa ta Facebook ne a watan fabairun shekara ta 2004 a ƙasar Amirka. Kuma wasu matasa uku wato Zuckerberg da Chris Hughes da kuma Moskovitz ne suka ƙirkiro shafin a wannan shekarar. Wanda dai akace ya jagoranci kafa shafin na Facebook tsakanin matasan dai shine Mark Moskovitz ɗan shekaru 23 a duniya dake karatun Sanin halayan ɗan Adam wato Psychology, a lokacin da yake ɗalibta a jami'ar Harvard dake ƙasar ta Amirka domin anfanin ɗaliban jami'ar.

Kafin kace kwabo wannan shafi ya samu ƙarɓuwa wajen sauran ɗalibai kimanin 1200 na jami'ar ta Harvard. Kuma cikin wata guda rabin ɗaliban dake karatun ƙaramin digiri na jami'ar sunyi rajista da shafin na Facebook. Haka dai wannan shafi ya rinƙa samun karɓuwa daga ɗalibai daga wannan jami'a zuwa wancan.

A shekarar 2005 ne kuma aka yiwa shafin rajista a matsayin facebook.com akan kuɗi Dalar Amirka dubu ɗari biyu. A watan satumban shekara ta 2005 kuma shafin na facebook ya isa ƙasar Birtaniya kafin zuwa sauran ƙasashen duniya. Kuma kyauta ne dai ake rajistan shafin na facebook.

Amma kuma don gane da hanyoyin samun kuɗi kuwa. Shafin wanda ya zama kanfani na samun kuɗaɗen sa ne daga tallace tallace da manyan kanfanoni da ƙanana keyi domin sayar da hajar su ga masu anfani da shafin ta facebook. Yanzu dai kanfanin da aka fara da Dalar Amirka dubu ɗari biyu, kanfanonin sadarwa irin su Google da Yahoo sun taya shi akan kuɗi Dala biliyan 2, wanda kuma Mr. Zuckerberg yace albarka.

Mark Zuckerberg

A shekarar 2004 an fara wata shari'a tsakanin Zuckerberg da kuma wasu masu mallakan kanfanin yanar sadarwa ta Connect U, wa'yanda ke zargin Zuckerberg da sace basirar kanfanin su, a lokacin da suka nemeshi daya shirya masu tsarukan shafin sadarwan su, a matsayin sa na kwararre a harkar na'ura mai ƙwaƙwalwa a lokacin da dukkannin su ke ɗalibta a jami'ar ta Harvard koda yake tuni kotu tayi watsi da ƙarar a sabili da rashin cikken sheda a shekarar 2007. Kuma kamar yadda wani shafin sadarwa shima na Wekepidia ta bayar yanzu haka dai akwai miliyoyin jama'a dake anfani da shafin ta Facebook da yawan su ya haura miliyan 350 a duniya.