Jump to content

Filin Wasa Na Adokiye Amiesimaka

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Filin Wasa Na Adokiye Amiesimaka
Wuri
Coordinates 4°58′03″N 6°58′17″E / 4.9675°N 6.9714°E / 4.9675; 6.9714
Map
History and use
Opening2015
Wasa ƙwallon ƙafa

Filin wasa na Adokiye Amiesimaka filin wasa ne mai maitukar Amfani da yawa a Fatakwal, Najeriya, a ƙarshen birnin a unguwar Omagwa. Filin wasan yana ɗaukar mutane 38,000.[1]

An bude shi a ranar 19 ga Yuli shekarata 2015 tare da wasa tsakanin Najeriya da Congo a wasan share fagen shiga gasar Olympics ta Rio wanda aka kammala da ci 2-1 a kan Congo.[2]

Daga baya a wannan watan, 'yan wasan Firimiyar Najeriya Dolphins sun ba da sanarwar cewa za su buga ragowar kakar shekarar 2015 a filin wasa.[3]

Daga 25 ga Janairu zuwa 27 2019, an yi amfani da filin wasan don taron kwanaki 3 mai taken, Babban Taron Rayuwa tare da Fasto Chris Oyakhilome . An cika shi da cikakken iko kuma dubban mutane sun zauna a babban filin don wannan taron. Yana aiki azaman gida ga Rivers United.[4]

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]