Fred Agbedi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fred Agbedi
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 -
District: Sagbama/Ekeremor
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

ga Yuni, 2015 -
Rayuwa
Haihuwa 20 ga Faburairu, 1960 (64 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Frederick Yeitiemone Agbedi (An haife shi ranar 20 ga watan Febrariru, 1960) ya kasance mai ilimantarwa ne, kuma dan siyasa daga jihar Bayelsa. Yana ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka kirkiro jihar Bayelsa. Yana daga cikin kungiya mai karfi na yaren Ijo wanda suka sa aka kirkiri jihohi sabbi a Nijeriya.[1]

Farkon rayuwa da llimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifeshi a Aghoro, alkarya ne dake kusa da ruwa a karamar hukumar Ekeremor, a jihar Bayelsa. Ya halarci makarantar jihar Aghoro da 'Oproza Grammar School' Patani don karatunsa na Firamare da Sakandare. Ya mallaki ilimin NCE da kwarewa akan Turanci da Tarihi daga kwalejin Ilimi na Warri, jihar Delta. Har wa yau ya mallaki digiri na ilimi (B. Ed) a Turanci  daga Jami'ar Patakwal (University of Port Harcourt kuma yayi mastas dinshi a Public Administration a Jami'ar Abuja.[2]

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Abedi ya zama cikakken dan siyasaa a shekarar 1992 bayan ya shiga jam'iyyar (NRC) kuma ya zama sakataren ƙungiyar a kauyensu na Ekeremor.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]