Jump to content

Freddie Ljungberg

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Freddie Ljungberg
Rayuwa
Cikakken suna Karl Fredrik Ljungberg
Haihuwa Vittsjö (en) Fassara, 16 ga Afirilu, 1977 (47 shekaru)
ƙasa Sweden
Karatu
Harsuna Swedish (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa, model (en) Fassara da association football coach (en) Fassara
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Sweden national under-17 football team (en) Fassara1993-199340
  Sweden national under-19 football team (en) Fassara1994-199481
Halmstads BK (en) Fassara1994-19987910
  Sweden national under-18 football team (en) Fassara1994-199481
  Sweden national under-21 football team (en) Fassara1995-1998125
  Sweden national association football team (en) Fassara1998-20087514
Arsenal FC1998-200721646
West Ham United F.C. (en) Fassara2007-2008252
  Seattle Sounders FC (en) Fassara2009-2010372
  Chicago Fire FC (en) Fassara2010-2011152
  Chicago Fire FC (en) Fassara2010-2010152
Shimizu S-Pulse (en) Fassara2011-201280
  Celtic F.C. (en) Fassara2011-201170
Mumbai City FC (en) Fassara2014-201440
 
Muƙami ko ƙwarewa winger (en) Fassara
Nauyi 69 kg
Tsayi 175 cm
Kyaututtuka

Karl Fredrik "Freddie" Ljungberg (An haifeshi ranar 21 ga watan Aprilu, 1977), kwararren dan kwallon kafa ne dan asalin kasar Swidin kuma tsohon dan wasa ne da yayi ritaya inda yanzu yana daya daga cikin masu bada horo a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal. Sannan kwararren dan wasa ne dake buga gefe.

Ya fara rayuwar kwallon shi a kungiyar kwallon kafa ta Halmsdad sai dai ya karar da mafi yawan shekarun sa na kwallo a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal inda yaci gasar Premier league guda 2 kuma yaci gasar FA itama inda ya zura kwallo sau 2 a raga hada nasarar da ya samu a shekarar alif 2002. Bayan yabar kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, yaje kungiyoyi na kasashe irinsu Ingila, Skotland, Amurka, Japan da kuma kasar Indiya. Ya kasance kyaftin na kasar Swidin daga 2006 har zuwa lokacin da ya sanar da ajiye a yayin gasar UEFA Europa na 2008.

A fannin kasa kuma Ljumberg ya buga wasanni 75 inda ya wakilci kasar tashi a gasanni da yawa inda ya wakilci kasar tashi a gasar Euro na shekarar alif 2000, 2004, da kuma 2008 da kuma gasar cin kofin duniya na shekarar alif 2002 da kuma 2006. Shine jagora kuma kaftin a kungiyar kwallon kafa ta Swidin tun daga shekarar alif 2006 har zuwa lokacin da ya aje kwallo bayan gasar Euro da aka buga a shekarar alif 2008.[5]

Rayuwar Baya[gyara sashe | gyara masomin]

A haifeshi a ranar 21 ga watan Afrilu shekarar alif 1977 a Vittsjo zuwa Roy Alve Erling Ljumberg namallakin kasuwancin gine gine kuma mai kwalin Mastas a fannin Injiniyanci, da Elisabeth Bodil Ljumberg, ma aikacin ma'aikatar fannin aikace aikace ta kasar Swidin.[8]

A ranar 12 ga watan Satumba shekarar alif 1984 Ljumberg ya sake haihuwar wani dan kharl Oskar Filip.[9]. Ashekara ta alif 1982 iyalan Ljumberg aun bar Vittsjo suka koma Halmsdad. Da farko a cikin shekaru 5 dinnan amma sai yayi gardama da iyayenshi cewa beson zama a Halmsdad din. Iyayenshi suka amince inda suka medashi Halmsdad Bk inda yayi kwallo a kungiyar matasa a karkashin mai bada horo wato Olle Eriksson.[9]

Lokacin da Ljumberg yake da shekaru 5 zuwa shekaru 14, yayi aiki ne a karkashin mai Mai horaswa wato Olle Eriksson. Dan wasan yana da basira ga hikima sosai idan ka hadashi da sauran yaran.

Dan wasan ya lashe kyautar Socratis Brazillian na shekara inda mai horas da dan wasan ya bada gagarumar wajan daukakar dan wasan.[11]

Dan wasan yana da kwarewa a sauran Wasanni yanada kwarewa a fannin wasan Hoki da wasan ƙwallon hannu inda kwarewar dan wasan ta sanya aka kirashi cikin yan wasan da zasu wakilci kasa cikin yan kasa da shekaru 15.[11] amma saboda dan wasan yafi maida hankali wajan wasan ƙwallon ƙafa shiyasa duk yabar yin sauran wasannin.

Ljumberg yana maida hankali sosai a makaranta da kuma kwallo. Dan wasan yana da kokari sosai tana cin maki Sosai a makaranta inda ya samu maki 4.1 a ma'auni inda ya gama na 9th a cikin jerin daliban.[18]

Dan wasan ta tsallaka makarantar gaba wato ta gaba da sakandire. Ljumberg yana karantar Kimiyya da Fasaha da tattalin arziki saidai ya fuskanci matsala da matsin lamba da suka sanya yabar karatun ya maida hankalinsa a wajan kwallo.[19]

Rayuwar Kungiya[gyara sashe | gyara masomin]

Halmsdad

A shekarar alif 1989, dan wasan a lokacin yana dan shekara 12. Ljumberg ya shawo kan kungiyar kwallon kafa ta Halmsdad din da au matsar dashi daga P12 zuwa P14 wanda yana daya daga cikin dokar kungiyar. Ljumberg ya jona kungiya ta (B) a karkashin jagorancin Nord Stroam. Jajircewar dan wasan ta biya saboda bayan shekaru 3 aka daukeshi a cikin babbar kungiya.

Ljumberg ya fara buga wasa a matsayin kwararren dan wasa a ranar 23 ga watan Oktoba shekara ta alif 1994 a filin wasa na Allsvenskan da kungiyar kwallon kafa ta AIK. A shekarar alif 1995, Ljumberg ya buga wasanni 31 inda yaci kwallo ta farko a matsayin kwararren dan wasa. A wannan shekarar kungiyar kwallon kafa ta Halmsdad din ta lashe gasar Svenska Cupen. A shekarar alif 1997 ne kungiyar kwallon kafa ta Halmsdad din ta lashe gasar Allsvenska inda dan wasan ya zura kwallaye ya kuma taimaka akaci kwallaye a kungiyar. Ya buga wasanni 139 a kungiyar inda yaci kwallaye guda 16.

Bayan gudummawa da kuma haskawa da dan wasan yayi a kungiyar kwallon kafar ta Halmsdad din, kungiyoyi da yawa sun nuna sha'awar su ga dan wasan kamar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Barcelona, Aston Villa, Parma da kuma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.[16]

Arsenal

Ljumberg ya rattaba hannu a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a shekarar alif 1998 akan jumillar kudi £3m. Babban mai horaswa dan asalin kasar Faransa wato Arsene Wenger da mukarrabansa sun lura da dan wasan yayin da suka kalli wasan shi a talabijin inda ya wakilci kasar shi ta haihuwa wato Swidin a wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Ingila kuma suka samu nasara a wasan.[17]

Duk da cewa mai horaswar baiga wasanshi a fili ba amma yada yakinin dan wasan zai bada gudummawa sosai a gasar ta Premier League. Hakan yasa mai horaswar ya siyo shi ba tare da anjima ba. Kuma dan wasan ya nuna kanshi inda ya nuna kwazo sosai inda ya fara zura kwallo a raga a ranar 20 ga watan Satumba inda ya shigo daga baya a wasan da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United inda wasan ya tashi 3-0.[18]

Ljumberg yayi wasanni guda 21 a shekarar a dukkanin gasanni. dan wasan ta farko inda ya buga wasanni 43 a shekarar gaba da ya buga a shekarar alif (1999-2000).[19] Ljumberg ya rasa buga wasan karshe da kungiyar ta buga a gasar UEFA Cup wanda aka buga a shekarar alif 2000 inda ya tsallake wasan rauni da ya samu a awazarsa.[20] A karshen shekarar sa ta 3 sun kai matakin karshe a gasar FA cup inda ya buga wasan inda yaci kwallo 1 saidai daga baya kuma kungiyar kwallon kafa ta Liverpool.[21] Hakan ya zama karo na farko da ya zura kwallo a wasan karshe a kungiyar tashi ta Arsenal. Kuma hakan yasa dan wasan ya kafa tarihi a wasan. Saboda babu wani dan wasa daya taba cin kwallo a wasan karshe wanda ya kasance ba dan ƙasar bane sai Ljumberg din. Wasan ya kasance shine wasan karshe na farko da dan wasan ya buga a filin wasa na Millennium Stadium a garin Cardiff.

Mafi yawancin kokarin dan wasan shine a matsayin dan canji idan ya shigo daga baya a shekarar alif (2001-02) lokacin da suka lashe gasar Premier league ta farko da kuma gasar FA cup guda 2. Bayan tafiyar Pires jinya Ljumberg yaci kwallaye da yawa har karshen kakar, daga harda kwallon da yaci kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a wasan karshe inda suka samu nasara daci 2-0. A shekarar, Ljumberg yaci kwallaye masu birgewa kuma masu ban sha'awa da jan hankalin magoya baya. Daga ciki hada kwallon da yaci kungiyar hamayya wato kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a wasan da aka tashi 3-1 kuma dan wasan ya shigo ne daga baya.[22] Haka zalika yayi kokari sosai a wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a filin wasa na Anfield inda kungiyar ta samu nasara daci 2-1. A wasan ne dan wasan ya nuna kwarewa sosai inda ya jawo bugun daga kai sai mai tsaron raga wadda babban dan wasan kungiyar wato Thierry Henry yaci ƙwallon. Sai kuma kwallo ta 2 inda Pires ya dago mashi kwallon shi kuma ya saka kwallon a raga.[23] Ya kara cin wata kwallon a ragar kungiyar kwallon kafa ta Liverpool din sati ukku da suka wuce a filin wasa na Highbury inda wasan yakare canjaras 1-1.[24] Ljumberg ya karar da wannan kakar wasan inda yaci kwallaye 17 a duka gasanni. Ljumberg yaci kwallo a wasan karshe na gasar FA wanda hakan babbar nasara ce a gareshi inda kuma ya kafa tarihi mai kyau kasancewar rabon da wani yaci kwallo sau biyu a jere a wasan karshe na FA tun bayan shekaru 40.[25]

A shekarar alif (2002-03) dan wasan ya taimaka ma kungiyar tashi inda suka kai matakin wasan karshe a gasar FA cup sau 3 a jere. Yaci kwallo wadda ta ba kungiyar nasara a wasan kuaa da na karshe da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Sheffield United inda suka samu nasara daci 1-0.[26] Inda suka buga wasan karshe da kungiyar kwallon kafa ta Southampton inda Pires yaci ƙwallon da taba kungiyar nasarar lashe gasar inda aka tashi 1-0.[27]

San wasan ya fara cin kwallaye ukku ringis a wasa daya a wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Sunderland inda wasan ya tashi 4-0.[28]

A shekarar alif 2003-04 Ljumberg yayi wasanni guda 30 a wasan lig na shekarar inda kungiyar ta shafe wasannin lig din duka ba tare da anci nasara akan kungiyar ba har akayi musu lakani da "marassa buguwa".[29]

A shekarar ne yaci kungiyar hamayya wato kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur a filin wasa na Highbury.[30]

A shekarar alif (2004-05) Ljumberg ya buga wasan matakin karshe na gasar FA cup a karo na hudu inda aka sanyoshi daga baya kuma yaci kwallo daya daga cikin jerin bugun daga kai sai mai tsaron raga da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United inda suka samu nasara akan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United din.[31].

an wasan yana buga ta fannin gefe ko kuma wani lokacin kuma yana buga tsakiya, wani lokacin ma yana buga gaba ta tsakiya.

Dan wasan ya zama daya daga cikin jerin 11 na farkon wasa da ake fitowa dasu kullum bayan tashin wasu yan wasa na ƙungiyar sune Emmanuel Petit da kuma Marc Overmars wadanda suka tashi a shekarar alif 2000. A shekaru masu yawa dan wasan ya buga wurare da yawa kuma yana cikin jerin yan wasan da suka buga wasanni 49 ba tare da an doke su ba a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal. Dan wasan yayi fama da raunuka a cikin rayuwar kwallon shi inda yayi dama da jinya na lokuta da dama. A shekarar alif 2005 ya samu rauni wanda ya kai ga matakin ciwon Cancer inda aka gano. Dan wasan yana fama da guba a jininsa sakamakon yawan zanen dake jikinsa.[32]

Dukda rauni da ɗan wasan ya samu a kafarsa amma ya buga wasa na matakin karshe da kungiyar ta buga da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai da aka buga a ranar 17 ga watan May shekarar alif 2006.[33]

A shekarar alif 2007 an yaɗa cewa an tilasta wa dan wasan yabar kungiyar kwallon kafa ta Arsenal saboda gajiya da masu bada horo na kungiyar sukayi saboda yawan jinya da dan wasan yakeyi inda suke ganin cewa salon wasan dan wasan ya fara canzawa kuma ya rage kokari sosai. Mai horar da kungiyar wato Arsene Wenger yace dan wasan yana da aiki sosai a gabansa.

A ranar 13 BnHa ga watan Junairu shekarar alif 2007 bayan wasan da aka buga da kungiyar kwallon kafa ta Blackburn Rovers karshen kaka wannan shine ya tabbatar da tsayawa da yayi har karshen kwantiragin nasa a shekarar alif 2009.[34][35]

Ljumberg ya dawo bayan doguwar jinya da yayi inda ya dawo a wasan gasar FA da aka buga da kungiyar kwallon kafa ta Bolton Wanderers inda ya zura kwallo a raga tun cikin mintuna 13 kafin aje karin lokaci inda ya sama wuri a zagaye na 5 a gasar inda suka hadu da kungiyar kwallon kafa ta Blackburn Rovers a zagaye na 5 a gasar.[36]

Dan wasan ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa Tottenham Hotspur a ranar 21 ga watan Aprilu 2007 wanda hakan ya tabbatar da barin dan wasan daga kungiyar.[37]

A shekarar alif 2008 an zabi dan wasan a mataki na 11 cikin jerin manyan yan wasa guda 50 na tarihin kungiyar.[38]

West Ham United

A ranar 23 ga watan Yuli shekarar alif 2007 Ljumberg ya koma ƙungiyar hamayya ta Landan wato kungiyar kwallon kafa ta West Ham United da yarjejeniyar kwantiragi na shekaru hudu.[38]

Ljumberg ya fara buga wasanshi na farko a shekarar alif 2007-08 inda sukayi da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City inda sukayi rashin nasara daci 2-0. A wasan shine ya daura Captain. Bayan watanni bakwai da yayi a kungiyar daga karshe ya zura kwallo a raga a wasan da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Birmingham City. A ranar 9 ga watan Fabrairu shekarar alif 2008, ya.zura kwallo a ragar kungiyar kwallon kafa ta West Ham United inda wasan ya tashi 1-1.[40] Sai kuma kwallo daya sa acikin ragar kungiyar kwallon kafa Sunderland.[41]

Ljumberg yaci gaba da taka leda a kungiyar kwallon kafa ta West Ham yayin da ya taimaka ma kungiyar tashi sosai inda yaci kuma ya taimaka akaci kwallaye da suka taimaka wajen samun nasara a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta West Ham United din.[43]

Akwai majiyar da tace an yima dan wasan tayin £3million domin ya yaga kwantiragin sa daya rage. Sai dai dan wasan bai amince da wannan tayin mai tsoka ba. Dan wasan ya ajiye wasa s kasar tashi. A cewar dan wasan shine yanaso ya maida hankali a kungiyar tashi ta West Ham United.

Daga karshe dan wasan ya cimma yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Elefalk akan jumillar kudi 6million

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]