Jump to content

Gabriel Magalhães

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Gabriel magalhaes)
Gabriel Magalhães
Rayuwa
Cikakken suna Gabriel dos Santos Magalhães
Haihuwa São Paulo, 19 Disamba 1997 (26 shekaru)
ƙasa Brazil
Karatu
Harsuna Portuguese language
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Avaí Futebol Clube (en) Fassara2016-ga Janairu, 2017342
  ES Troyes AC (en) Fassara2017-201810
  Brazil national under-20 football team (en) Fassara2017-201770
Lille OSC (en) Fassaraga Janairu, 2017-30 ga Augusta, 2020392
  GNK Dinamo Zagreb (en) Fassara2018-201810
  Brazil Olympic football team (en) Fassara2020-202140
Arsenal FC1 Satumba 2020-unknown value11211
  Brazil national football team (en) Fassara2023-61
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya
Lamban wasa 6
Nauyi 78 kg
Tsayi 190 cm

Gabriel dos Santos Magalhães An haifeshi a ranar 19 ga watan Disamba 1997 wanda aka fi kiranshi da suna Gabriel. Kwararren dan wasan kasar Brazil ne wanda yake taka leda a matsayin dan baya. Dan wasan ya kasance yana buga gasar premier league ta ingila, inda yake taka leda a kungiyar Arsenal. Sannan kuma babban dan wasa ne da yake wakiltar kasar brazil.

Rayuwar kwallo[gyara sashe | gyara masomin]

Avai

An haifi dan wasan ne a Prituba District na Sao paulo. Tun yana da shekaru goma sha ukku 13, ya fara doka ma kungiyar ta avai wasa. Saidai kuma ya dawo Saulo saboda yawan jinya ta gida. Sai dai ya kuma sake dawowa Avai din bayan wasu yan satuttuka. Ya fara rattaba hannu a matsayin kwararren dan wasa a shekaru 16. Yajevwata kungiya ne wadda ta samu damar tsallakewa zuwa babbar gasa ta Brazil a shekarar alif dubu biyu da goma sha bakwai 2017.

Lille

A ranar 31 ga watan Junairu 2017 dan wasan ya koma taka leda a Gasar League 1 inda yake taka leda a kungiyar lille inda ya rattaba hannu da kwantiragin shekaru hudu da rabi. Lokacin da ya isa a garin, ya koya ma kansa yaren faransaci saboda mafi yawancin tattaunawa da ake dashi da faransaci akeyi. Bayan ya buga wasanni da yawa a kungiyar ta lille, ya ya tafi zaman aro a kungiyar troyes. Kafin ya koma kungiyar dake kasar Croatia wato dynamo zegreb inda ya buga wasa daya kacal a kowace kungiyar.

Dan wasan ya dawo lille 2018 inda ya fara wasanshi na farko a ranar 10 ga watan Fabrairu 2019 a wasan da ya buga da kungiyar hamayya Guingamp wadda tayi rashin nasarar ketarawa gasa ta kasanta inda suka samu nasarar lashe wasan daci 2-0. Dan wasan yaci kwallonsa ta farko ne inda suka fafata da kungiyar P. S. G, inda suka zazzaga ma P. S. G din kwalaye har 5-1 wanda aka buga a 14 April 2019.

Shekara ta gaba, ya zama mai doka wasanni a koda yaushe kuma ko wane wasa za a buga dole sai ansashi matukar anaso a samu nasara a wasan.

Arsenal

A ranar 1 ga watan September 2020 Arsenal suka wallafa a shafinsu na daukar dan wasan da yarjejeniyar kwantiragi mai tsawo da akayi da dan wasan da kuma kungiyar. An sayi dan wasan da jumillar kudi kimanin £27m.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

"2020/21 Premier League squads confirmed". Premier League. 20 October 2020. Retrieved 21 October 2020.

  1. ^ Jump up to:a b
  2. ^ "GABRIEL MAGALHÃES FORA DA COPA DO MUNDO. "SE ISSO FOI COLOCADO NA BALANÇA É UM ABSURDO!"" [GABRIEL MAGALHÃES OUT OF THE WORLD CUP. "IF THIS WAS PUT ON THE SCALE IT IS ABSURD!"]. YouTube (in Brazilian Portuguese). De Placa. 13 July 2023. Retrieved 25 October 2023.