Geberit

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Geberit

Bayanai
Iri kamfani da public company (en) Fassara
Masana'anta plumbing (en) Fassara
Ƙasa Switzerland
Aiki
Bangare na Swiss Market Index (en) Fassara da Natur-Aktien-Index (en) Fassara
Mulki
Hedkwata Rapperswil-Jona (en) Fassara
Tsari a hukumance Aktiengesellschaft (en) Fassara
Financial data
Haraji 2,910,000,000 Fr (2017)
Stock exchange (en) Fassara Swiss Stock Exchange (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 1874

geberit.com


hoton geberit
hoton heberit

Geberit ( lafazi a harshen Jamusanci: [ˈɡeberɪ:t ] ƙungiya ce ta ƙasar Switzerland wacce ta ƙware a sarrafawa da kuma samar da kayan kula da jiki da dai makamantansu. Ma'aikatar ta kasance majagaba fagenta a Turai tare da rassanta a ko ina a fadin duniya.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Geberit hedkwatar.

Farkon Farko[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin shekarar 1874, Caspar Melchior Gebert ya fara kasuwancin kayan famfo a Rapperswil, Switzerland. A 1905, ya fara kera sassan kayan. Tankin masai, Fonix, na farko, wanda aka yi da itace mai lullube da karfen lead (musamman mai magudada), ya kasance cigaba ne kuma babban nasara. Lokacin da Gebert ya mutu a shekara ta 1909 'ya'yansa Albert da Leo sun karbi kasuwancin. A cikin shekaru masu zuwa, kamfanin ya fadada a fadin Switzerland da kuma zuwa makwabta kasashe, kuma sun kara sababbin samfurori (bututai, famfuna da bawuloli). A cikin shekarun alif 1930s, kamfanin ya kasance majagaba a samar da sassa na filastik a tsakanin masana'antun kayan tsaftace muhalli.

Yaƙin Duniya na biyu ya shafi kamfanin, amma ba da daɗewa ba kamfanin ya murmure kuma a shekarar 1952 ya gabatar da tankin masai na farko da aka yi da polyethylene.

Fadadawa[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 1953, Heinrich da Klaus Gebert sun gaji shugabancin kamfanin kuma sun sanya masa suna Geberit. Kamfanin ya bude rassan rarraba kaya da kuma sabbin rassa a Turai, kuma suna bada hidimomi na musamman. Kamar yadda ake ɗaukar kasar Jamus a matsayin cibiyar kasuwanci, an buɗe rukunin farko na ƙasa da ƙasa a can a cikin 1955, a Pfullendorf, wanda kuma zai kasance wurin da masana'anta na farko a wajen kasar Switzerland. Tun daga wannan lokacin, an ƙirƙiri wasu rassa a ƙasashen Turai, ciki har da Faransa (1959) da Austria (1965). Kamfanin ya tashi daga Rapperswil zuwa wani babban wuri a Rapperswil-Jona kuma sun gabatar da tsarin tanki dake a ɓoye.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]