Geneviève Aclocque
Geneviève Aclocque | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Léopoldine Marcelle Geneviève Aclocque |
Haihuwa | 2nd arrondissement of Lyon (en) , 5 Mayu 1884 |
ƙasa | Faransa |
Mutuwa | Saint-Antoine-du-Rocher (en) , 28 ga Augusta, 1967 |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Joseph de Croy (en) (11 Satumba 1933 - |
Karatu | |
Makaranta | École des chartes (en) 1910) archivist palaeographer (en) |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | Masanin tarihi da medievalist (en) |
Kyaututtuka |
gani
|
Mamba |
Société de l'École des chartes (en) Société de l’histoire de France (en) Société de l'histoire de Paris et de l'Île-de-France (en) |
Geneviève Aclocque (Léopoldine Marcelle Geneviève Aclocque) (biyar ga watan Mayu 1884 - ashirin da takwas ga Agusta 1967) yar tarihin Faransa ce. [1]
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Geneviève Aclocque a ranar biyar ga watan Mayu 1884 a Lyon. A cikin shekarar 1906, Ta zama mace ta farko da aka shigar da ita a École Nationale des Chartes. Ta sauke karatu a shekarar 1910. [2]
A cikin shekara ta 1917 ta buga "binciken tarihi na kasuwanci a Chartres." Dokar masu yin ulu a Chartres ta ba wa mata damar shiga kasuwanci.[3] A cewar Aclocque, matakan farko na samar da ulu sun kasance ne ta hannun ma'aikatan maza, yayin da mata ke yin amfani da distaffs.[4] Har ila yau, akwai wata al’ada ta yadda ƙwararrun masu saƙar ulu a Chartres za su iya koya wa magadansu, namiji ko mace, don maye gurbinsu a matsayin ƙwararrun sana’a. [5][4]
Binciken nata ya kuma nuna alaƙa tsakanin ayyukan kasuwanci da wasu al'adu na addini. Bugu da kari wallafe-wallafenta sun yi iƙirarin cewa don gujewa ko da rage haraji, ma'aikatan gidan abinci sun sayar da giyan su a cikin tashar Chartres.
Ta auri ɗan tarihi Joseph de Croy. Ta mutu a ranar ashirin da takwas ga watan Agusta 1967 a Saint-Antoine-du-Rocher.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Geneviève Aclocque (1884-1967)" (in Faransanci). BnF. Retrieved 2 May 2022.
- ↑ Ha, Marie-Paule (2014). French Women and the Empire: The Case of Indochina. Oxford: Oxford University Press. p. 210. ISBN 978-0-199-64036-2. Retrieved 2 May 2022.
- ↑ Welch Williams, Jane (1993). Bread, Wine, and Money: The Windows of the Trades at Chartres Cathedral. Chicago: University of Chicago Press. p. 4. ISBN 978-0-226-89913-8. Retrieved 2 May 2022.
- ↑ 4.0 4.1 Burns, E. Jane (2006). "Saracen Silk and the Virgin's "Chemise": Cultural Crossing in Cloth" (PDF). Speculum. 81 (2): 365–397. doi:10.1017/S0038713400002621. Retrieved 2 May 2022.
- ↑ Burns, E. Jane (14 July 2014). Sea of Silk: A Textile Geography of Women's Work in Medieval French Literature. Philadelphia: University of Pennsylvania Press. p. 233. ISBN 978-0-812-29125-4. Retrieved 2 May 2022.