Gerald Takwara
Gerald Takwara | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | Harare, 29 Oktoba 1994 (30 shekaru) | ||||||||||||||||||
ƙasa | Zimbabwe | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||
|
John Gerald Tungamirai Takwara ,(An haife shi a ranar 9 ga watan Oktoba a shekara ta 1994) . ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Zimbabwe wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron gida a ƙungiyar Venda ta Afirka ta Kudu, da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Zimbabwe.
Sana'a/Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Takwara ya fara aikinsa a kasarsa ta Zimbabwe da Tsholotsho Pirates da FC Platinum, kafin ya koma Afirka ta Kudu da Ajax Cape Town. Ya koma Zimbabwe tare da Ngezi Platinum, kafin ya koma Afirka ta Kudu tare da Venda a ranar (22) ga watan Yuli a shekara ta (2021).[1]
Ayyukan kasa
[gyara sashe | gyara masomin]Takwara ya fara buga wasansa na farko na kasa da kasa tare da tawagar kasar Zimbabwe a (0–0) a shekara ta (2016) a gasar cin kofin kasashen Afirka da Comoros a ranar (4) ga watan Yuli a shekara ta (2015).[2] Ya kasance cikin tawagar 'yan wasan Zimbabwe a gasar cin kofin Afrika na shekara ta (2021).[3]
Girmamawa
[gyara sashe | gyara masomin]FC Platinum
- Gasar Premier ta Zimbabwe : 2017
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Gerald Takwara confirms return to SA PSL". 22 July 2021.
- ↑ Strack-Zimmermann, Benjamin. "Comoros vs Zimbabwe (0:0)". www.national-football-teams.com
- ↑ Afcon 2021: A Zimbabwe squad is named despite threat of a FIFA ban". BBC Sport. 29 December 2021.
Hanyoyin haɗi na waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Gerald Takwara at National-Football-Teams.com
- Gerald Takwara at Soccerway